Labarai

Shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ya rasu

Shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ya rasu

Shugaban Ohanaeze Ndigbo, Emmanuel Inwuanyanwu ya rasu. Sanarwar ta fito daga bakin ɗan sa, Jude Inwuanyanwu inda ya ke cewa" a madadin iyalan Inwuanyanwu, na Umoahii Atta da ke ƙaramar hukumar Ikeduru a Jihar Imo, muna sanar da mutuwar shugaban mu, baban mu, kuma jagora, Eng Emmanuel Inwuanyanwu" Inwuanyanwu ya rasu ne ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli bayan wata gajeruwar rashin lafiya. Kafin mutuwar tashi, shine shugaban ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo. Inwuanyanwu jagora ne da ke faɗa a ji a yankin nasu, kuma babban ɗan kasuwa ne, kuma mai mallakin sananniyar jaridar nan ta Champion Newspaper.
Read More
An fara gina sabuwar matatar mai a Legas duk da rikicin Matatar Ɗangote

An fara gina sabuwar matatar mai a Legas duk da rikicin Matatar Ɗangote

DUK da ce-ce-ku-ce tsakanin matatar Dangote da hukumomin kula da harkokin matatar man fetur ta Najeriya, a ƙarshe, Midoil Refining and Petrochemicals Company Limited ya samu damar gudanar da bikin ƙaddamarwa, wanda yake nuni da fara ayyukan ginin matatar a jijar Legas. An gudanar da bikin ƙaddamarwan ne a Shekungba, a karamar hukumar Ikosi/Ejinrin da ke jihar Legas kwanan nan. Shugabar kamfanin na Midoil, Mrs Elizabeth-Omolara Akintonde, ta jagoranci manyan mutane zuwa ga filin gurin, wanda ya ratsa al’ummomi da dama a karamar hukumar Ikosi/Ejinrin. Akintonde ta tabbatar wa shugabanni da al'ummomin cewa matatar man za ta kawo sauyi a…
Read More

Gwamnatin Tinubu ta yi barazanar garƙame mahandaman shugabannin ƙananan hukumomi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi barazanar gudanar da bincike kan shugabannin ƙananan hukumomi da su ka sauya akalan kuɗaɗen asusun ƙasafi na ƙasa (FAAC). Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya faɗi hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron ƙungiyar Marubuta Ƴancin Ɗan-adam inda ya ce duk wanda aka samu da laifin handame ƙuɗin ƙaramar hukuma, to za a kulle shi a kurkuku. Idan ba a manta ba, a ranar 11 ga watan Yuli ne kotun ƙoli ta yi hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: DSS ta sako matasan da ta kama kan shirin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta sako Injiniya Khalid Aminu da Sanusi Aliyu waɗanda ta kama su a kwanakin baya kan zargin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wa laƙabi da 'EndBadGovernance'. Sanarwar haka ta fito daga Omoyele Sowere, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar AAC a zaɓen 2023 a wani rubutu da ya yi a kafar sadarwa. An kama Khalid ne a safiyar ranar Alhamis don zargin gayyato mutane shiga zanga-zangar gama-garin a jihar Kaduna, yayin da a irin haka aka kama Sanusi a ranar Talata a jihar Sakkwato, 23 ga watan Yuli. Rahotanni…
Read More
INEC za ta iya zaɓukan ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasa – Farfesa Yakubu Mahmud

INEC za ta iya zaɓukan ƙananan hukumomi a duk faɗin ƙasa – Farfesa Yakubu Mahmud

Makonni biyu bayan da kotun ƙoli ta bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu a Najeriya, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar zaɓen na iya samun nasarar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin idan doka ta ba su dama. Shugaban na INEC ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki kan harkokin zaɓe domin gabatar da kasafin kuɗin zaɓen Ondo da Edo a ranar Alhamis. Mahmood ya bayyana cewa, hukumar da a halin yanzu take gudanar da zaɓuka ba tare da tangarda ba…
Read More

Zanga-zanga: Masu amfani da wayoyi da motoci ake hari, DHQ ta gargaɗi al’umma

Daga BALA MUHAMMAD Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), ta ce ta gano wani shiri da wasu ɓata-gari ke yi na kai hari wa masu motoci da masu amfani da manyan wayoyi da kuma mallakar wasu kadarori a cigaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar 'EndBadGovernance' a za a yi wata mai zuwa. A ranar Alhamis ne, Daraktan ofishin kan harkokin yaɗa labarai, Manjo Janar Edwerd Buba ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda ya ce sun gano akwai maƙarƙashiya da ka iya haifar da tarzoma a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa mutane da dama na goyon…
Read More
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma Wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, ya yaba da amincewa da Ƙudurin, ya ce amincewar shugaban ƙasa za ta samar da hukumar da za ta sa baki a ɓangaren gwamnatin tarayya sannan za ta magance taɓarɓarewar ababen more rayuwa a yankin. Jibril ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Talata cewa, hukumar za ta rage wahalhalun ababen more rayuwa a yankin da Boko Haram da ‘yan bindiga suka lalata. Ya cigaba da cewa, “Abin da shugaban…
Read More
Gwamnan Zamfara ya jinjina wa Tinubu kan amincewa da ƙudirin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Gwamnan Zamfara ya jinjina wa Tinubu kan amincewa da ƙudirin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Daga USMAN NASIR KAROFI Gwamna Dauda Lawal ya jinjinawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ya sanya hannu a kan ƙudurin ƙirƙirar hukumar ci gaban Arewa maso Yamma A wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Gwamnan ya yi matuƙar jinjinawa Shugaban domin yin hakan zai kawo cigaba mara adadi ga yankin. Ya bayyana cewa, hukumar an ƙirƙire ta domin ayyuka irin su gina tituna, gidaje da kasuwanci da suka rushe a yankin. Ya cigaba da cewa, yin haka tabbas zai kawo sauƙi ga raɗaɗin talauci da ake fama dashi. Ya jinjina…
Read More
Mu riƙa tuhumar gwamnoni kamar yadda mu ke tuhumar Tinubu – Ramat

Mu riƙa tuhumar gwamnoni kamar yadda mu ke tuhumar Tinubu – Ramat

Tsohon Shugaban ƙaramar Ungoggo, Eng Abdullahi Garba Ramat yayi kira da mutanen gari su rinƙa tuhumar gwamnonin jihohin su kamar yadda suke tuhumar Shugaban ƙasa Tinubu. Yayi wannan bayanin a shafin sa na dandalin Facebook, inda ya ke cewa tunda a ka cire tallafin mai, yawan kuɗin da jihohi suke samu ya ninka sama da kaso 50, yace ma jihohi irin su Nasarawa, ninki ya kai kaso 100. Ya faɗa cewa, idan akwai waɗanda ya kamata ayi wa zanga-zanga, gwamnoni ne ba Shugaban ƙasa ba. Ya cigaba da bada misali ya na cewa, ƙaramar hukuma kamar Ungoggo a watan Yuni,…
Read More
Kamfanin Meta ya rufe shafuka aƙalla 63,000 domin daƙile satar yanar gizo

Kamfanin Meta ya rufe shafuka aƙalla 63,000 domin daƙile satar yanar gizo

Daga USMAN KAROFI a Abuja Meta Platforms Inc, kamfanin da ke da Instagram da WhatsApp ya sanar a ranar Laraba cewa za a cire wasu shafuka 63,000 da ke da alaƙa da masu aikata laifuka ta yanar gizo a Nijeriya, waɗanda ke damfarar kuɗi a yayin amfani da shafukan. A cikin rahoton kamfanin na 2024 a ranar Laraba, Meta ya bayyana cewa shafukan da aka cire sun kai kimanin 63,000 a yayin wani binciken haɗin gwiwa da kamfanin ya gudanar. Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya gano tare da cire waɗannan shafuka ta hanyar amfani da fasaha na zamani da…
Read More