Labarai

Zanga-zangar Tsadar rayuwa: Ƙungiyar matasa ta umarci rassanta 104 su kasance a shirye

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A cigaba da shirye-shiryen zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi a watan Agusta, Ƙungiyar matasa ta ƙasa, NYCN ta umarci ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin ta da su kasance cikin shiri ganin cewa kwanakin na ƙara kusantowa. Sanarwar ta fito daga shugaban ƙungiyar, Sukubu Sara-Igbe Sukubu cikin wata takarda da ya fitar biyo bayan wani taron gaggawa da shugabannin rassan ƙungiyar na Jihohi 36 suka gudanar ta kafar Zoom a rana Alhamis inda ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda al'ummar Nijeriya ke fama da matsanancin rayuwa musamman matasa. Cikin matsalolin da matasan ke buƙatar gwamnati ta…
Read More
Ya kamata a ba matatar Ɗangote dukkan goyon baya – Kwankwaso ya shawarci Tinubu

Ya kamata a ba matatar Ɗangote dukkan goyon baya – Kwankwaso ya shawarci Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Laraba ne tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso ya yi la’akari da rashin jituwar da ke tsakanin hukumar kula da matatar man Ɗangote da hukumomin da ke kula da harkokin man fetur NMDPRA a Nijeriya Hukumomin Nijeriya sun zargi matatar Ɗangote da fitar da gurɓataccen man fetur mara inganci, iƙirarin da kamfanin ya musanta. Da yake mayar da martani a shafinsa na Ɗ, Kwankwaso ya ce ya kamata gwamnatin Nijeriya da ba matatar dukkanin goyon baya don bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, domin yin barazana ga matatar a cewarsa ka iya sage wa…
Read More
Ƙungiya ta yaba wa AGILE don inganta ilimi a Gombe

Ƙungiya ta yaba wa AGILE don inganta ilimi a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe A ƙoƙarinta na haɗa kai da AGILE don bada gudummawarsu wajen ci gaban ɓangaren ilimi a jihar Gombe, wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba mai suna Open Knowledge Deɓelopment Initiatiɓe ta yaba da yadda ake gudanar da aikin AGILE a Jihar Gombe. Yabon ya fito ne daga bakin Daraktan ƙungiyar Open Knowledge Deɓelopment Initiatiɓe, Adamu Usman Garko, wanda ya jagoranci tawaga zuwa sashin gudanar da aikin a Gombe. Adamu Garko ya ce ziyararsu ta samo asali ne sakamakon abubuwan da aka tsara a aikin da suka shafi inganta ilimin 'yan mata matasa a…
Read More
Ƙungiyar ƙwararru ta ƙasa reshen Jihar Kano sun gudanar da taro don haɓaka ci gaban jihar

Ƙungiyar ƙwararru ta ƙasa reshen Jihar Kano sun gudanar da taro don haɓaka ci gaban jihar

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Gwamnatin Jihar Kano a shirye take ta karɓi shawarwari daga ƙwararru domin haɓaka ci gaban Jihar Kano da al'ummarta. Kwamishinan ma'aikatar ayyuka, Injiniya Marwan Ahmad  ne ya bayyana hakan a taron ƙungiyar   ƙwararu na ƙasa  reshen Jihar Kano da aka gudanar a ɗakin taro na Mambayya. Ya ce Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ƙofar ta a buɗe yake wajen karɓar shawarwari da zai ciyar da Kano gaba daga irin wannan ƙungiyar ta ƙwararru  Ya ce irin muhimman batutuwa da ya ji an tattauna a taron zai yi  mutuƙar taimakawa Gwamnati idan…
Read More
Na yi zanga-zanga a baya amma ta lumana, inji Tinubu

Na yi zanga-zanga a baya amma ta lumana, inji Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da cewa ya sha shiga cikin masu zanga-zanga daban-daban amma ba ta tashin hankali ba. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi takardar amincewa daga sabon jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr. a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Ya kuma jaddada muhimmancin ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya, yana mai cewa zanga-zangar wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya, amma babu wata gwamnati da za ta amince da zanga-zangar da zai iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Shugaban ya ce, “Dangartakarmu da Amurka tana da kyau. Mun yi imani…
Read More
Zanga-zanga: Babu abinda ya haɗa ku da harkar farar hula – Effiong ga sojoji

Zanga-zanga: Babu abinda ya haɗa ku da harkar farar hula – Effiong ga sojoji

Wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Inibehe Effiong, ya ce rundunar sojin Nijeriya ba ta da wani hurumi na fitar da sanarwa kan wani lamari na farar hula. Masanin shari'ar ya ce, babu wanda zai tsorata da barazanar ta su. Sanarwar ta zo ne bayan hedikwatar tsaro ta gargaɗi masu gangamin zanga-zangar a faɗin ƙasar cewa ba za ta lamunci rashin zaman lafiya ba. Kamar aka sani, wasu ’yan Nijeriya na shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agustan 2024 domin nuna adawa da matsayin…
Read More
Yaƙi da yunwa ya fuskanci koma-baya na shekaru 15 – Majalisar Ɗinkin Duniya

Yaƙi da yunwa ya fuskanci koma-baya na shekaru 15 – Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (SOFI) ta ce, cigaban yaƙi da yunwa a duniya ya fuskanci koma-baya a cikin shekaru 15, wanda ya bar kusan mutane miliyan 733 ke fama da yunwa a cikin 2024. Wannan adadi, ya ce ya yi daidai da ɗaya cikin mutane 11 a duniya da kuma ɗaya a cikin biyar a Afirka, a cewar sabon rahoton Hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (SOFI) da aka buga ranar Laraba. Rahoton na haɗin gwiwa ne na FAO, da asusun bunƙasa noma na ƙasa da ƙasa (IFAD), da asusun kula da ƙananan…
Read More
Jam’iyyun adawa ne suka shirya zanga-zangar matsin rayuwa, inji Wike

Jam’iyyun adawa ne suka shirya zanga-zangar matsin rayuwa, inji Wike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi zargin cewa 'yan adawa ne suka ɗauki nauyin gudanar da zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin aasar. Wike, wanda ya bayyana hakan bayan duba aikin titin Apo-Karshi a ranar Talata, ya ce matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita ba Shugaba Bola Tinubu ne ya jawo ta ba. Yayin da yake neman a ƙara haƙuri, Mista Wike ya ce gwamnati mai ci tana tunkarar ƙalubalen da ta gada daga magabata. “Mu gaya wa kanmu gaskiya mai sauƙi. Idan muna siyasa, a ce muna siyasa; idan…
Read More
An buƙaci Wike da Sufeto Janar su hana rusau a kasuwar Mpape

An buƙaci Wike da Sufeto Janar su hana rusau a kasuwar Mpape

’Yan kasuwa a Tsohuwar Kasuwar Mpape da ke Ƙaramar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja sun kai ƙara ga Sufeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike bisa cigaba da rusa gine-ginen kasuwar da hukumar ke yi. Masu shagunan da abin ya shafa sun koka da cewa, ayyukan rushe-rushen da Majalisar Ƙaramar Hukumar Yankin Bwari ke aiwatarwa ta hanyar Hukumar Kiyaye Muhalli ta Abuja (AEPB) ta yi sanadiyar salwantar ɗimbin dukiya, asarar rayuka da rusa rayuwar jama’a, ba tare da wani nau’i na diyya ko wani shiri na daban ga ’yan kasuwar…
Read More

A na zargin Matawalle da taimaka wa Yahaya Bello wajen tserewa zuwa Nijar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A na zargin ƙaramin ministan tsaro, Muhammed Bello Matawalle da shirya ficewar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ake zargi da sama-da-faɗi da dukiyar al'umma daga Nijeriya zuwa Jamhuriyar Nijar da taimakon jami'an tsaro. Wani ɗan jaridar bincike mai suna Jackson Ude ya faɗi haka ta kafar X a ranar Alhamis. Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello da aka zarge shi da handame sama da Naira biliyan 80 a lokacin da ya ke gwamnan Kogi inda ya yi ta ƙoƙarin kaucewa kamawa da kuma bincike. Ɗan jaridar…
Read More