Labarai

Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe ya rantsar da kansiloli 13

Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe ya rantsar da kansiloli 13

Daga GAMBO ISA Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a jihar Yobe, Hon. Alhaji Baba Goni Mustapha Bade ya rantsar da sabbin zaɓaɓɓun kansiloli 13. Da yake jawabi a wajen taron da babbar kotun majistare ta gudanar a zauren majalisar da ke Damagum, bisa ga kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya Hon. Baba Goni Mustapha Bade ya miƙa saƙon taya murna ga sabbin zaɓaɓɓun kansilolin, inda ya jaddada muhimmancin ayyukansu, wajen yin aiki tuƙuru da inganta ruhin aiki bisa ƙa'idojin majalisar ƙaramar hukumar da aka kafa. Wannan taron dai wani gagarumin ci gaba ne a tafiyar ƙaramar hukuma Fune, inda ya yi nuni…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Obama ya goyi bayan Kamala Haris ta zama Shugabar Amurka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya goyi bayan ƴar takara Kamala Haris ta yi nasara a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe bayan da shugaban Joe Biden ya ƙudiri aniyar janyewa daga tsayawa takara. Sanarwar ta fito ne a ranar Juma'a, kwanaki kaɗan da Kamala ta shelanta tsayawarta takarar kujerar shugabancin ƙasar. Wata ɗaukar bidiyo, ta nuna yadda Obama ya kira ta a waya, yana mai cewa shi da matarsa, Michelle suna goyon bayan ta tare yi mata alƙawarin samun gudunmawarsu ga kai wa nasararta. 'NBC News' ta ruwaito cewa, kasancewar Obama shi ne baƙin…
Read More

Ƙungiyoyin Islama sun buƙaci a hana ɗaukar sanya hijabi da sunan fashi a cikin fina-finai

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƴancin al'ummar musulmi (MURIC) da cibiyar lamuran al'ummar musulmi (MPAC) sun buƙaci a ɗauki tsauraran matakai ciki har da dakatar da wani fim da ke nuna mata sanye da niƙabi ɗauke da muggan makamai suna fashi a bankuna da laifuka masu kama da haka. Jawabin ya fito ne daga mabanbanta ofisoshi a ranar Alhamis da su ka haɗa da Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola da shugaban MPAC, Disu Kamor. A kwanan nan ne tauraruwar masana'antar 'Nollywood', Nancy Isime ta yaɗa hotunan ɗaukar fim ɗin da ake shirin fito da shi a yanar gizo waɗanda su…
Read More
Usman Adamu ya yi Allah-wadai da tsarin rabon taki wa manoman Nasarawa

Usman Adamu ya yi Allah-wadai da tsarin rabon taki wa manoman Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Wani babban manomi kuma shugaban al'umma dake garin Agyaragu a jihar Nasarawa mai suna Alhaji Usman Adamu da aka fi sani da Doya-hamsin ya bayyana rashin jin daɗinsa a madadin manoman jihar bakiɗaya game da tsarin da aka bi aka raba takin noma wa manoman jihar wadda gwamnatin jihar ta gudanar kwanan nan. Alhaj Usman Adamu Doya-hamsin ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da rabon takin na bana inda ya bayyana cewa “Da farko dai tambaya da ka min magana ne babba kuma in ka ga gaskiya ka…
Read More
Ba mu janye daga zanga-zangar da za a gudanar ba  – NLC

Ba mu janye daga zanga-zangar da za a gudanar ba – NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC ta musanta raɗe-raɗin cewa ta janye daga zanga-zangar ƙasa da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta. Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Ɗ, NLC ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya tare da cewa ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ita ta shirya ba. “Masu shirya zanga-zangar ta ƙasa ce kawai za su iya yanke shawarar janyewa ko ci gaba da zanga-zangar,” in ji NLC. Sanarwar ta bayyana cewa “NLC tana da hanyoyi musamman hanyoyin yanke hukunci kan jagoranci wanda ayyukanta…
Read More
Wasu sojojin Nijeriya sun koka kan rashin biyansu alawus

Wasu sojojin Nijeriya sun koka kan rashin biyansu alawus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A Nijeriya, wasu daga cikin sojojin ƙasar da ke ayyukan samar da tsaro a jihar Zamfara sun koka game da yawan jinkirin da ake samu, wajen biyansu kuɗaɗensu na alawus, inda suka ce akan biya su kuɗin wata guda ne kacal bayan kwashe watanni biyu ko uku, lamarin da ke jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a cewarsu. Sai dai hukumomin sojan Nijeriyar sun ce suna sane da wannan ƙalubale da ke gaban dakarun da ke fagen daga, amma ana ƙoƙarin shawo kan lamarin nan ba da daɗewa ba. Wasu sojojin da suke aiki ƙarƙashin…
Read More
Majalisar Kaduna ta soke Hukumar Kula da Manyan Biranen jihar

Majalisar Kaduna ta soke Hukumar Kula da Manyan Biranen jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dokokin Kaduna ta rushe dokar da ta kafa hukumar kula da biranen Zariya da Kaduna da kuma Kafanchan. A ranar Laraba Majalisar ta soke dokar da ta kafa hukumar wacce tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai ta ƙirƙiro a shekarar 2021. Majalisar ta ce ta soke dokar kula da biranen ne bayan hukuncin Kotun Ƙoli na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu. “Don haka yanzu babu buƙatar wannan hukumomi” da El-Rufai ya kafa a lokacinsa dake kula da biranen jihar. Dama dai dangantaka ta yi tsami a tsakanin tsohon El-Rufai da majalisar dokokin…
Read More

Ba ni da iyayen gida da zan sakawa, Inji Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kore zargin cewa ya na da waɗanda su ka dafa masa cikin ɗaiɗaikun mutane ko kuma wata ƙungiya a siyasarsa, yayin da ake cigaba da daidaita al'amuran tattalin arziƙi, ya ce shi ya ɗauki nauyin yawon neman zaɓensa ba tare da taimakon wasu mutane ko ƙungiyoyi ba. Tinubu wanda ya karɓi baƙoncin malaman addinin Islama ƙarƙashin jagorancin Sheikh Bala Lau a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, ya ce nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa iko ne na Ubangiji da kuma shiri na tsanake tare da samun goyon bayan ƴan Nijeriya. Shugaba Tinubu…
Read More
Burtaniya za ta kashe sama da fan miliyan 10 don aikin mayar da baƙin haure Rwanda

Burtaniya za ta kashe sama da fan miliyan 10 don aikin mayar da baƙin haure Rwanda

Gwamnatin Burtaniya ta shirya kashe aƙalla Fan biliyan 10 ƙarƙashin sabon tsarin aikin kwashe baƙin haure tare da jibge su a Ƙasar Rwanda kamar yadda ƙasashen biyu suka kulla yarjejeniya. Sakatariyar harkokin cikin gida ta ƙasar Yɓette Cooper ta ce tuni har an tattara Fan miliyan 700 cikin kuɗin daga hannun masu biyan haraji. Cooper ta kuma ce waɗannan kuɗaɗe sun haɗa da kuɗin jirgin da zai yi jigilar su, biyan ma’aikatan da zasu sanya idanu wajen ganin an maida su Rwanda, da kuma biyan gwamnatin Rwanda kan wannan aiki da zata yi. Sabon Prime ministan wasar Keir Starmer wanda…
Read More

Nijeriya ta sayo man fetur ɗin Dala 2.25bn daga Malta, kwanaki kaɗan da Ɗangote ya zargi akwai ma su ɓoyayyun masana’antun mai a ƙasar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwanaki kaɗan bayan da shugaban matatar mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi zargin cewa akwai jami'an kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC da ke da ɓoyayyun masana'antun mai a ƙasar Malta, alƙaluma sun bayyana cewa Nijeriya ta sayo man fetur na tsabar kuɗi da adadinsa ya kai Dala biliyan 2.25 daga ƙasar. Wata sanarwa daga 'Trade Map', ta ce a shekarar 2023, Nijeriya ta shigo da man fetur na Dala biliyan 2.8 wanda hakan ya haura da kashi 342 a kan na Dala miliyan 47.5 da aka sayo a shekarar 2013. An gano cewa,…
Read More