Labarai

DSS ta sake kama wani matashi kan shirya zanga-zanga a Sakkwato

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar Ƴan sandan farin kaya ta DSS, ta yi nasarar kama wani matashin Nijeriya mai suna Aliyu Sanusi kan shirya zanga-zangar da ke ƙalubalantar raunin shugabanci a faɗin ƙasar. An kama matashin ne a yammacin ranar Litinin, a hanyar Sama da ke Sakkwato, babban birnin jihar. Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowere ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar Talata inda ya buƙaci hukumar ta gaggauta sako matashin, yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka. Lamarin ya auku ne bayan da DSS ta sako wani matashin mai suna Bashir…
Read More

Rundunar ‘Yan sanda ta roƙi mazauna Abuja kar su shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kwamishinan 'Yan sandan birnin tarayya, Abuja, Bennet Igweh ya roƙi al'ummar jihar kar su shiga zanga-zangar da aka shirya za a yi a watan Agusta kan tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Igweh ya nuna damuwarsa kasancewar ɓata gari ka iya amfani da zanga-zangar wajen tarwatsa sabbin ayyukan cigaba da a ka yi a faɗin jihar. Kwamishinan, ya bayyana hakan ne a yayin hira da manema labarai a ranar Litinin a lokacin da rundunar ta gurfanar da mutane da dama kan zargin fashi a hedkwatar ofisoshinta da ke birnin. Ya ce, suna aiki tuƙuru wajen kamo ƴan…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya aika da ƙudurin sabon mafi ƙarancin albashi majalisa

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya aika da ƙudurin sabon mafi ƙarancin albashi majalisa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da ƙudurin dokar mafi ƙarancin albashi ga majalisar wakilai domin tantancewa tare da amincewa da shi. An karanta wasiƙar Tinubu a zauren majalisar a yau Talata, inda ya tanadi sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma tsarin doka na aiwatar da albashin idan aka amince da shi. A cikin wasiƙar, shugaban ya buƙaci ‘yan majalisar da su gaggauta amincewa da ƙudurin dokar mafi ƙarancin albashi domin tabbatar da aiwatar da shi cikin gaggawa domin amfanin ma’aikatan Najeriya. Tinubu ya kuma nemi kwaskwarima ga dokar ‘yan sandan Nijeriya kamar yadda sashe na 58…
Read More

‘Yan sandan Kano sun kama fursunan da ya tsere daga kurkukun Kuje, wanda ya kitsa kashe janar na soja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda ta yi nasarar kama wanda aka zarge shi da kitsa kisan marigayi Burgediya Janar Harold Udokwere, mai suna Hashiru Baku wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere daga kurkukun Kuje a kwanakin baya. Jaridar 'News Point Nigeria' ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka shiga gidan janar Harold tare da kashe shi a unguwar rukunin gidajen Sunshine da ke Abuja a ranar 21 ga watan Yuni, inda Ƴan sanda ƙarƙashin kwamishinan rundunar Abuja, Bennet Igweh su ka kama waɗanda ake zargi kwana biyu bayan aukuwar lamarin. A lokacin da aka gurfanar da ƴan…
Read More

ASUU ta janye yajin aikin Jami’ar Abuja da aka ɗauki kwanaki 82 ana yi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jami'ar Abuja ɓangaren ƙungiyar malaman jami'o'i ta sanar da dakatar da yajin aikin da aka ɗauki tsawon kwanaki 82 ana yi inda ta ce nan da nan za a dawo bakin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Sylvanus Ugo ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai bayan kammala wani zama na ƙungiyar a Abuja inda ASUU tare da majalisar zartarwar Jami'ar su ka tattauna yayin da majalisar ta yi alƙawarin yin duba ga buƙatunsu tare da samar musu da mafita a kan su. A ranar biyu ga watan Mayu, 2024 ne aka shiga yajin aikin sakamakon…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta jagoranci ganawa kan taƙaddamar matatar Ɗangote da NMDPRA

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawa kan taƙaddamar da ke tsakanin hukumar man fetur ta NMDPRA da sabon matatar Ɗangote wanda ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya jagoranta wanda Alhaji Aliko Ɗangote da shugabannin NMDPRA suka halarta. An shirya zaman ne da nufin wanzar da haɗin kan ɓangarorin biyu da kuma warware ɓoyayyun matsalolin da ka iya shafar ayyukan matatar wanda ake tsammanin hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen dogaro da dangogin mai daga ƙasashen waje da Nijeriya ke yi. Wata takarda da mai bai wa ƙaramin ministan shawara kan yaɗa labaru, Nneamaka Okafor, ya…
Read More
Wani ɗan sanda da ke cikin maye ya harbe mahaifinsa a Borno

Wani ɗan sanda da ke cikin maye ya harbe mahaifinsa a Borno

Wani ɗan sanda ya harbe mahaifinsa, ASP Wadzani Ntasiri, wanda ya kasance mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) mai ritaya, bayan wani saɓani da su ka yi ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Sajan ɗan sandan wanda aka bayyana sunansa da Linus Wadzani, ma’aikacin tsaro ne a harabar majalisar dokokin jihar Borno. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke Maiduguri, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), ASP Nahum Daso, ya ce mahaifin ɗan sandan da ya kashe shi ya yi aiki da rundunar…
Read More
Wani jirgin Max Air ya samu fashewar taya yayin da yake shirin tashi

Wani jirgin Max Air ya samu fashewar taya yayin da yake shirin tashi

Jirgin Max Air mai lamba NGL1649, Boeing 737 mai lamba 5N-ADB, ɗauke da fasinjoji 119 da ma’aikata shida, ya gamu da haɗari kwatsam a lokacin da ya ke ƙokarin tashi a filin jirgin Yola a yammacin Lahadi. A wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a , Bimbo Oladeji, ya fitar, jirgin ya samu matsala ne bayan an bashi damar tashi shi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Yola a jihar Adamawa, kan hanyarsa ta zuwa Abuja. A cewar sanarwar, “Lokacin da ake shirin tashi, an ji ƙara mai karfi, wanda aka gano cewa tayoyi ne na baya suka…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙirƙiro dokar Iddah ga zawarawa

Gwamnatin Katsina ta ƙirƙiro dokar Iddah ga zawarawa

Gwamnatin jihar Katsina ta ɓullo da dokar Iddah, domin baiwa mata ma’aikatan gwamnati damar zama a gida na tsawon wata huɗu da kwana goma idan sun rasa mazajensu. A musulunce ana yin iddah lokacin da mace ta rasa mijinta. Gabatar da sabuwar dokar ya biyo bayan wani ƙuduri da Majalisar Dokokin jihar ta gabatar, inda ta buƙaci gwamnatin jihar da ta duba batun wa’adin Iddah wanda hukumar zartaswa ta amince da shi, tare da yin aiki da shawarwarin da ‘yan majalisar zartaswa suka gabatar. Shugaban ma’aikatan Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman…
Read More
Sojoji sun sake ceto  wata ‘Yar Chibok mai ‘yaƴa biyu

Sojoji sun sake ceto wata ‘Yar Chibok mai ‘yaƴa biyu

Daga USMAN KAROFI a Abuja Rundunar haɗin gwiwa a yankin Arewa maso Gabas mai suna " Operation Haɗin Kai", ta ceto wata ‘yar Chibok daga dajin Sambisa a Jihar Borno. Kwamandan rundunar, Manjo Janar Waheed Shuaibu ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa ta da ‘ya’yanta biyu ga gwamnatin Jihar Borno a unguwar Maimalari da ke Maiduguri, ranar Litinin. A cewarsa, Ehi Abdul, mai shekaru 27, ta auri wani fitaccen dan ta’adda, Abu Dada a Gwoza a shekarar 2014, ya kuma tsere zuwa ƙasar Senegal. Wani sashe na rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ da ke dajin Sambisa ne suka…
Read More