Labarai

’Yan sanda sun kama wasu mutane bisa zargin saka wa yara wiwi a fanke

’Yan sanda sun kama wasu mutane bisa zargin saka wa yara wiwi a fanke

Wasu mutaum biyu na fuskantar tuhuma kan yunƙurin kisan kai a Afirka ta Kudu bayan da wasu yara kusan 90 suka kamu da rashin lafiya bayan cin fanke da aka sanya wa tabar wiwi. Jami’ai sun ce yaran sun sayi fanken ne a wajen wani mutum a gefen titi a kan hanyarsu ta zuwa makarantar firamare ta Pulamadibogo, a arewa maso yammacin Pretoria. An kai da dama daga cikinsu asibiti saboda tashin zuciya da ciwon ciki da kuma amai. An zargi mutanen biyu masu shekaru 21 da kuma 19 da yunƙurin aikata kisa a ranar Juma’a. Ma'aikatar ilimi ta lardin…
Read More
Tasgaron zuwan turawa Ƙasar Hausa

Tasgaron zuwan turawa Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da irin alfanu da muka zayyana waɗanda suka samu a Ƙasar Hausa sakamakon zuwan Bature, ba kuma za a rasa tasgaro, cigaban mai haƙar rijiya, da kuma koma baya waɗanda zuwan Turawa ya haifar ba. Tabbataccen abu ne a tsarin rayuwa, cewa, duk lokacin da aka samu sauyi ko cuɗanya da wasu baƙin jama’a, waɗanda tasirinsu ya kai ga wata jama’ar ta sauya salon yadda take gudanar da rayuwarta, babu makawa, sai an samu abubuwan da za su saɓa da abin da yake karɓaɓɓe  a tafarkin rayuwar waɗannan jama’a da aka zo aka taras. Zuwan…
Read More
Shugabannin addinai sun fi jami’an gwamnati aikata almundahana – Shugaban EFCC

Shugabannin addinai sun fi jami’an gwamnati aikata almundahana – Shugaban EFCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati, EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kakkausar suka ga fastoci da limamai, inda ya ce wasu daga cikinsu sun fi jami’an gwamnati cin hanci da rashawa. Olukoyede, wanda ya yi magana a wani taron shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da aka gudanar a Legas ranar Juma’a, ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC ta ƙwato miliyoyin Naira daga hannun wata ƙungiyar addini kwanan nan. Ya ce, “Bayan naɗi na, na yi tunani a kan matsayina na shugaban hukumar da sakatariyar hukumar. Na gane cewa ɗaya…
Read More
Har yanzu ni ɗan haya ne a Abuja – Ɗangote

Har yanzu ni ɗan haya ne a Abuja – Ɗangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiayr Afirka, Aliko Ɗangote ya bai wa jama'a da dama mamaki tun bayan da ya sanar da cewa ba shi da gida a ƙasashen waje. Ɗangoto ya kuma sanar da cewa gidajensa biyu ne rak sannan kuma gidan haya yake sauka a duk lokacin da ya je Abuja, babban birnin Nijeriya. Ta ƙara da cewa, “Ban taɓa ganin wanda ya kai mahaifina aiki tuƙuru ba, wani lokacin ina mamakin yadda ba ya kasala. "Ina fata muna da wasu maza kamar mahaifina a Nijeriya, ƙasar za ta yi kyau," inji…
Read More
Afam Osigwe ya zama shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya

Afam Osigwe ya zama shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya

Afam Osigwe wanda shine tsohon sakataren ƙungiyar lauyoyin Nijeriya ya zama sabon shugaban ƙungiyar a zaɓen da aka gudanar. Zaɓen an yi shi ne ta hanyar yanar gizo. Zaɓen ya fara ne tun 12 na safiyar Asabar zuwa 11:59 na ranar Lahadi. Osigwe yayi nasara samun ƙuri'u 20,435, yayin da wanda yayi na biyu ya samu ƙuri'u 10,998. Osigwe zai amshi shugabancin ne daga hannun Yakubu Maikyau(SAN) wanda wa'adin mulkin shi ya zo ƙarshe. Sebatian Anyia shine ya zamo mataimaki na farko na ƙuri'u 12,114. Sai kuma Bolatumi Animashaun ya zama mataimaki na biyu da ƙuri'u 26,534. Yayin da Zainab…
Read More

Zanga-zangar tsadar rayuwa: Ya kamata gwamnati ta yi abin da ya dace – Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA Shugaban gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG), Kwamared Jamilu Aliyu Charanci, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su tashi tsaye su yi duk mai yiwuwa domin hana abin da ke shirin faruwa a ƙasar. Kwamared Aliyu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira a cikin makon nan, a lokacin da ake tsaka da batun gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar harkar tsaro da ake fama da su musamman a Arewacin ƙasar. Shugaban ƙungiyar ya ce, sanin kowa ne al'umma tana cikin…
Read More
Yadda Kirista ya kula da mahaifiyata a hannun masu garkuwa

Yadda Kirista ya kula da mahaifiyata a hannun masu garkuwa

Shahararren mawaƙin Hausa, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana yadda wani Kirista da aka yi garkuwa da shi ya ɗauki nauyin kula da mahaifiyarsa, Hauwa Adamu, a lokacin da ake tsare da ita wajen masu garkuwa.Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an sako mahaifiyar tashi mai shekaru 75 a ranar Alhamis bayan ta shafe kusan makonni uku a hannun wanda su ka yi garkuwa da ita.A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta a ranar Asabar, Rarara ya godewa ‘yan Nijeriya bisa addu’o’i da fatan alheri da suka yi a lokacin da mahaifiyarsa ta…
Read More

Rikicin APC a Zamfara: Marafa ya naɗa kwamitin jagorancin jam’iyyar na ɓangarensa

Daga SANUSI MUHAMMAD A. GUSAU A ranar Asabar ne Sanata Kabiru Garba Mafara ya kafa kwamitin mutum 21 na jam'iyyar APC mai kula da ɓangarensa a jihar Zamfara. Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron sirri da mambobin kwamitin, shugaban kwamitin, Hon. Surajo Maikatako ya bayyana cewa rashin adalci da kyakkyawan shugabancin jam’iyyar da shugaban Jam'iyar ke yi a jihar ne ya jawo rabuwar ɓangaren Sanata Kabiru Garba Marafa. A cewarsa, kwamitin zai bai wa haɗin kai da cigaban jam’iyyar muhimmanci a jihar, yana mai jaddada cewa kwamitin zai yi bakin ƙoƙarinsa wajen ganin an yi…
Read More
Ba hurumin Fadar Shugaban Ƙasa ba ne hukunta Sanata Ndume da Ningi – Ministan Labarai

Ba hurumin Fadar Shugaban Ƙasa ba ne hukunta Sanata Ndume da Ningi – Ministan Labarai

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayyar Nijeriya ta wanke Fadar Shugaban Ƙasa ko Ɓangaren Zartarwa na Tarayya baki ɗaya tana mai cewa, ba su da hurumin dakatar da Sanata Ali Ndume ko Sanata Abdul Ningi, waɗanda Majalisar Dattawa ta hukunta su a kwanakin baya.A yayin da ya ke amsa tambayoyi a kafar yaɗa labarai ta BBC a ƙarshen mako, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan, ya na mai cewa, ko kusa babu hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukunce-hukuncen da Majalisar Dattawa ta yi wa ‘ya’yan nata.Ya ce, “na farko ka ga…
Read More
Bambancin gwamnatin Tinubu da sauran shine ta yarda akwai matsala – Idris

Bambancin gwamnatin Tinubu da sauran shine ta yarda akwai matsala – Idris

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, bambancin ta da sauran gwamnatocin baya shine, ta yarda kuma ta amsa cewa, akwai matsaloli da suke addabar al’ummar ‘yan Nijeriya, waɗanda suke buƙatar a gaggauta shawo kansu saɓanin yawancin gwamnati a ƙasar da ba su iya fitowa su amince da cewa, akwai matsalolin. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a zantawarsa da BBC a ƙarshen makon nan.Idris, wanda ya ke amsa tambaya kan halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki, ya ce, “na farko bari…
Read More