Labarai

Gamayyar ƙungiyoyin Ƙwadago za su ɗau mataki ga duk jihar da ta gaza biyan mafi ƙarancin albashi

Gamayyar ƙungiyoyin Ƙwadago za su ɗau mataki ga duk jihar da ta gaza biyan mafi ƙarancin albashi

Ƙungiyar ƙwadago reshen Jihar Osun, ta ce za ta ɗau mataki a kan duk jihar da ta gaza biyan mafi ƙarancin albashin ₦70,000. Wannan ya fito ne daga bakin Mr Christopher Arapasopa a wata hira da yayi da manema labarai a birnin Osogbo. Ya ƙara da cewa, a ƙungiyar ta ƙwadago ta amshi wannan ₦70,000 domin gujewa ƙarin farashin mai. Wanda yace, in haka ya faru to ƙarin albashi ba zai yi wani amfani ba, zai jefa yan Nijeriya cikin wata wahalar ba ma'aikata kaɗai ba. Ya cigaban da faɗa, babu wani gwamna da zai ce ba zai iya biya…
Read More

An umarci bankuna su tura ƙuɗaɗen asusun da aka daina amfani da su ga CBN

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An umarci bankunan Nijeriya da cibiyoyin harkokin kuɗi su mayar da ƙuɗaɗen asusun da aka daina amfani da su da waɗanda ba a bayyana mallakar su ba da wasu kadarori ga babban bankin Nijeriya, CBN. Jawabin ya fito ne cikin wani saƙon umarni da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan sashen tsarin kuɗaɗe da gudanar da bankuna, John Onojah inda ya ce duk asusun da ƙuɗaɗen da ba a bayyana mallakar su ba da suka kai shakara goma, za a gadar da su ga asusu mai suna; 'Unclaimed Balances Trust Fund Pool Account' (UBTF). Bankin ya…
Read More

TCN ya yi barazanar sauke kamfanin lantarki na Abuja daga tashar wuta ta ƙasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin raba wutar lantarki na ƙasa, TCN, ya aika saƙon dakatarwa ga kamfanin lantarkin Abuja, AEDC kan zargin ƙin biyayya ga dokokin kasuwa. TCN ya ce, AEDC ya gaza samar da tsarin gudanar da kasuwa da isasshen tabbacin shaidar banki kamar yadda sakin layi na 15.3.3 na dokar kasuwanci ya nuna. Haka nan, an sanar da AEDC batun matsalar kuma an bashi kwanakin aiki biyar ya gyara ko kuma a sauke shi daga tashar. Jawabin ya ƙara da cewa, wa'adin zai ƙare ne a ranar 28 ga watan Yuli, da tsakiyar dare. Kazalika, AEDC ya sha…
Read More

‘Yan bindiga sun kashe sarki da ɗansa a Taraba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu ƴan bindiga a jihar Taraba sun kashe Sarkin Chanchanji, Mai girma Alhaji Tanimu Kunbiya da ɗansa, Yusuf Tanimu a lokacin da su ke dawowa daga ta'aziyya daga ƙaramar hukumar Takum a raɓar Juma'a. Wata sanarwa daga ofishin mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai, Emmanuel Bello ta ce, gwamna Agbu Kefas ya samu labarin aukuwar lamarin tare da ta tausaya wa waɗanda ya shafa inda nan take ya bada umarnin gudanar da bincike domin gano makasan tare da alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki. Gwamnan ya jaddada cewa, za…
Read More
Hukumar DSS ta kashe da kama waɗanda suka yi garkuwa da mahaifiyar Mawaƙi Rarara

Hukumar DSS ta kashe da kama waɗanda suka yi garkuwa da mahaifiyar Mawaƙi Rarara

Jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya sun kashe ɗaya tare da kama wani daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasan nan, Dauda Rarara. In bamu manta ba, wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan mahaifiyar Rarara da ke ƙauyen Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da ita a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni, 2024. Sai dai ta samu 'yanci bayan ta shafe kwanaki 20 a tsare. Wata majiya mai ƙarfi a hukumar ta shaida wa Jaridar Aminiya cewa an kuma gano Naira miliyan 26.5 a wani samame…
Read More

Shugabannin Majalisar Wakilai sun ziyarci matatar Ɗangote

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tawagar shugabannin Majalisar Wakilai ta ziyarci matatar Ɗangote da ke Lekki a jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Tajudeen Abbas. Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kuma shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote da wasu manyan ma'aikatan matatar su ka tarbi tawagar inda ƴan majalisar yayin dubiyar matatar da ka iya fidda ganga 650,000 a kullum. Wannan shi ne karo na biyu da su ke ziyartar matatar cikin wata biyu ganin cewa tana shirin fara aikin samar man fetur a wata mai zuwa da kuma ƙalubale da take samu daga kamfanonin kasashen waje kan…
Read More
Zanga-zanga: Ana so a yi amfani da matasa wajen ɓata sunan yankinmu  – Hon El-Abuja

Zanga-zanga: Ana so a yi amfani da matasa wajen ɓata sunan yankinmu  – Hon El-Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar 'APC Northwest Ambassadors', Hon Shamsudden Shu'aibu El-Abuja ya gargaɗi al'ummar Arewacin Nijeriya musamman matasa akan zangar-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi ƙarshen wannan watan. Hon. Shu'abu El-Abuja ya ce ana son yin amfani da al'ummar yankin Arewa ne kawai wajen ɓata sunan yankin, inda ya nuna cewa dole matasa suka zuciya nesa tare da ƙara juriya da haƙuri. "Idan matasan Nijeriya musamma 'yan Arewa  suka yi nazari, kawai ana son yin amfani da mu ne wajen ɓata sunan yankinmu. "Nasan cewa kun yi haƙuri iya haƙuri, kun raka amma har yanzu…
Read More
MDD ta nemi gaggauta cimma muradun ci gaba mai ɗorewa don cimma burin 2030

MDD ta nemi gaggauta cimma muradun ci gaba mai ɗorewa don cimma burin 2030

Ko’odinetan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ya kammala ziyarar aiki ta mako guda a Jihohin Legas, Enugu, da Anambra, inda ya yi kira da a gaggauta samar da ci gaba mai ɗorewa don cimma burin 2030. Sanarwar wacce ke ƙunshe a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na cibiyar yaɗa labarai ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Oluseyi Soremekun, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da aka fitar da rahoton muradun ci gaba mai ɗorewa na 2024, wanda ya bayyana cewa kashi 17 cikin 100 ne kawai na manufofin SDG…
Read More
Yadda wasu jami’oi ke ba ‘yan ƙasa da shekara 10 gurbin karatu

Yadda wasu jami’oi ke ba ‘yan ƙasa da shekara 10 gurbin karatu

Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bankaɗo badaƙalar da wasu jami'oi ke yi na karya dokar shekarun masu neman shiga manyan makarantun Najeriya. Oloyede ya bayyana cewa wasu jami’o’in na karɓar ɗalibai tun suna ƙasa da shekara 10, inda suka saɓa ƙa’idar da doka ta ƙayyade na shekaru 18. Da yake jawabi yayin taron manufofin JAMB a Abuja, Oloyede ya buga misali da jami’o’i kamar UNILAG da OAU, wadanda ke da ƙarancin shekarun da ake buƙata na shekaru 16 kafin a ba mutum gurbin karatu Ya kuma bayar da labarin wata ɗaliba da ta nemi…
Read More
Yadda aka kama wasu ‘yan luwaɗi a Gombe

Yadda aka kama wasu ‘yan luwaɗi a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama matasa biyu da ake zargi da aikata luwaɗi. Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Yulin 2024, rundunar ta samu labarin cewa an kama waɗanda ake zargin suna saduwa da juna ta dubura a unguwar Kanbariki da ke garin Kumo. Daga nan rundunar ta je wuri ta cafke waɗanda ake zargin inda aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu. Buhari ya bayyana cewa a lokacin da ake gudanar da bincike waɗanda ake zargin…
Read More