Yadda wasu jami’oi ke ba ‘yan ƙasa da shekara 10 gurbin karatu

Spread the love

Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bankaɗo badaƙalar da wasu jami’oi ke yi na karya dokar shekarun masu neman shiga manyan makarantun Najeriya.

Oloyede ya bayyana cewa wasu jami’o’in na karɓar ɗalibai tun suna ƙasa da shekara 10, inda suka saɓa ƙa’idar da doka ta ƙayyade na shekaru 18.

Da yake jawabi yayin taron manufofin JAMB a Abuja, Oloyede ya buga misali da jami’o’i kamar UNILAG da OAU, wadanda ke da ƙarancin shekarun da ake buƙata na shekaru 16 kafin a ba mutum gurbin karatu

Ya kuma bayar da labarin wata ɗaliba da ta nemi digirin digirgir a wata jami’a a ƙasar Jamus, sai aka gano cewa ta kammala karatunta a jami’ar Nijeriya tana da shekara 15.

Ya ce: “Duk da cewa shekara 18 ne batun, amma UNILAG, OAU ba za ta yarda da duk wanda bai kai 16 ba. Wasun ku za su yarda ko da 10. Dubi misalin wadda ta nemi gurbin karatu a wata makaranta a Jamus. Erasmus Scholarship.

Kasar ta yi mamakin cewa an haifi ɗalibar a shekarar 2007 kuma a kan fasfo ɗin ta ta fara jami’a tun tana shekara 12. Kwamitin da ke da alhakin bada gurbin karatu, ya tuntubi Najeriya don tabbatar da ɗalibin ya yi karatu a jami’ar kuma ya kammala karatunsa yana da shekaru 15 a Najeriya.

By ukarofi