Labarai

NLC ta kira taron gaggawa kan cire hannu da FEC ta yi a batun mafi ƙarancin albashi

Daga Farouk Abbas Mambobin haɗaɗɗun ƙungiyoyin ƙwadago sun kira taron gaggawa jim kaɗan bayan da majalisar ministoci (FEC), ta sanar da cire hannunta kan batun mafi ƙarancin albashi da ake yi a Najeriya. Wani babban ma'aikacin ƙwadago ya ce za a gudanar da taron ne a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, a babban ofishin NLC, a ɗakin taro na 'Labour House' da misalin ƙarfe 10 na safe. Ma'aikacin ya bayyana cewa, za a yi taron ne musamman saboda hukuncin majalisar ministoci na cire hannu kan tattauna a batun mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata da ake tataɓurza a kai da…
Read More

Majalisar Ministoci ta cire hannunta kan batun mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar ministoci (FEC), ta ce ta janye daga tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashin ma'aikata, domin bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu damar cigaba da neman shawarwari da masu-ruwa-da-tsaki kan batun. Ministan harkokin yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Mohammed ya faɗi hakan a yayin hira da wakilan fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a ranar Talata. Idris ya ce, shugaba Tinubu ya yi nazari kan rahoton kwamitoci uku na tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashin, sannan kuma zai yi shawara da waɗanda lamarin ya shafa kafin miƙa sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar ƙasa.…
Read More

Gwamnan Sakkwato ya musanta shirin tuɓe Sarkin Musulmi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu ya musanta zargin da ƙungiyar ƴancin musulmin Najeriya (MURIC), ta yi na cewa yana shirin tuɓe Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III daga kujerarsa. A kwanakin baya ne babban daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya tada batun, inda ya ce gwamnati Jihar na shirin korar Sultan Sa'ad Abubakar daga muƙaminsa la'akari da rikicin Masarauta da ke cigaba da aukuwa a Jihar Kano. Farfesan ya yi gargaɗin cewa, al'ummar musulmi a Najeriya ba za su amince da hukuncin sauke Sarkin ba inda ya ce Sarki Sa'ad ba Sarkin gargajiya ba…
Read More
Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto

Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto

Daga Umar Garba a Katsina Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto game da wasu rahotanni dake bayyana cewar gwamnatin jihar ta tura wata doka zuwa majalisar dokokin jihar wadda za ta rage wa Sarkin Musulmi ƙarfin iKon da yake da shi ko kuma ta kore shi daga kan kujerar ta sa. " Sarkin Musulmi ba na Sokoto ba ne kawai ba, kujera ce wadda wajibi ne dukkanmu mu kare ta, mu ɗaukaka ta don amfanin ƙasa." Inji shi.Shettima ya bayyana haka ne a wajen taron haɗin gwiwa wanda gwamnonin jihohin arewa maso yamma haɗin gwiwa…
Read More

A guji amfani da maganin ‘B-GAG’ – Hukumar NAFDAC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da dokar abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta yi kira ga ƴan Najeriya da su guji saya ko amfani da wani magani mai suna 'B-GAG' na ruwa, sakamakon shiga kasuwa da ya yi ba tare da cike ƙa'idoji ko yin rijista da hukumar ba. Bayanin ya fito ne daga ofishin darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye a wata takardar sanarwa mai lamba 023/2024 a ranar Lahadin da ta gabata inda ta ce, ana sayar maganin wanda ba a tantance ko yi masa rijista ba daga wani kamfani mai suna 'Babban Gida Agalawa…
Read More

Iyalan ɗalibin sekandiren NAF da aka kashe sun buƙaci a yi adalci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Iyalai da wakilan cocin wani mataimakin shugaban daliban makarantar sekandire ta rundunar sojin sama (NAF) da ke Kaduna, Felix Blaise da aka kashe, sun buƙaci hukuma da ta yi adalci yayin binciken kisan Ɗalibin mai shekaru 15, ɗan aji biyar, ana zargin an kashe shi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda wata jarida ta yanar gizo ta ce wasu ɗalibai su biyu ƴan aji shida ne suka sa masa lantarki wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. NAF ta ce, tana cigaba da bincike kan lamarin domin gano haƙikanin abun da ya faru. Haka nan, wakilin cocin…
Read More
Sojoji sun kuɓutar da mutane 98 daga hannun yan ta’adda, cikinsu har da ƴar Chibok

Sojoji sun kuɓutar da mutane 98 daga hannun yan ta’adda, cikinsu har da ƴar Chibok

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da aƙalla mutane 98 daga hannun yan ta'adda, cikinsu harda yarinya ɗaya daga cikin yan matan Chibok da akai garkuwa dasu shekerun baya. Anyi wannan nasarar ne a wani atisayen soja mai taken " Operation Lake Sanity II" wanda cigaba ne daga atisayen baya mai taken "Operation Hadin kai" Wasu bayanai na sirri da Zagazola, ƙwararre a harkar tsaro ya samu ya nuna yar Chibok ɗin da aka ceto itace mai lamba ta 64 a cikin jerin sunayen yan matan Chibok ɗin da akai garkuwa dasu.
Read More

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a kisan wani babban soja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar Ƴan sanda ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi kan kisan tsohon shugaban rundunar soji na ƙasa kuma jami'i Mai ritaya, Burgediya Janar, Harold Udokwere. Jaridar 'Blueprint' ta ruwaito cewa an kashe babban sojan ne a gidansa dake layin Sanga, a rukunin gidajen Sunshine, a unguwar Lokogoma dake Abuja a yayin wani fashi da wasu ƴan bindiga suka kai yankin. An samu bayanin ne a wani faifan bidiyo da ke ɗauke da rubutu inda waɗanda aka kama sun haɗa da; Ibrahim Rabi'u, mai shekaru 33 daga Ƙaramar Hukumar Dala, Jihar Kano mazaunin Rasha Apo…
Read More
‘Ƴan bindiga sun kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo

‘Ƴan bindiga sun kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo

'Ƴan bindiga sun kashe mataimakin Shugaban Jami'ar Usmanu Dan fodio Farfesa Yusuf Saidu. A litinin ɗin yau makarantar ta fitar da sanarwa cewa hakan ya faru ne a kan hanyar shi daga Kaduna zuwa Sokoto. Sanarwar ta ce " mutuwar Farfesa Saidu Yusuf, Mataimakin Shugaban Jami'ar a kan ƙirkire ƙirƙire da cigaba na Jami'ar" Hukumar makarantar ta bayyana mutuwar shi a matsayin wani babban rashi ga makarantar, suna addu'a Allah ya jiƙanshi, yayi mashi rahama.
Read More