NLC ta kira taron gaggawa kan cire hannu da FEC ta yi a batun mafi ƙarancin albashi

Spread the love

Daga Farouk Abbas

Mambobin haɗaɗɗun ƙungiyoyin ƙwadago sun kira taron gaggawa jim kaɗan bayan da majalisar ministoci (FEC), ta sanar da cire hannunta kan batun mafi ƙarancin albashi da ake yi a Najeriya.

Wani babban ma’aikacin ƙwadago ya ce za a gudanar da taron ne a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, a babban ofishin NLC, a ɗakin taro na ‘Labour House’ da misalin ƙarfe 10 na safe.

Ma’aikacin ya bayyana cewa, za a yi taron ne musamman saboda hukuncin majalisar ministoci na cire hannu kan tattauna a batun mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata da ake tataɓurza a kai da ta yi.

Jaridar ‘Daily Trust’, ta ruwaito cewa, ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Idris Mohammed ya ce an ɗauki batutuwa 39, inda batun mafi ƙarancin albashi ne kaɗai ba a ɗauka ba a wani taro da suka gabatar

Ministan ya ce akwai rahoton kwamitocin ƙungiyoyin ƙwadago tun daga matakin ƙananan hukumomi, Jihohi da ma gwamnatin tarayya da ya ƙunshi batun mafi ƙarancin albashi wanda akwai matakin tattauna shi.

Idris Mohammed ya ƙara da cewa, FEC ba za ta iya yin hukunci kan batun ba tunda akwai dukkan masu-ruwa-da-tsaki a ciki wanda ya haɗa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, don haka suka yanke shawarar barin shugaban ya tuntuɓi ofisoshin kafin miƙa hukuncinsa ga majalisar ƙasa, domin samun maslaha ga lamarin.

By Babaji