Labarai

Ƴan sanda sun ƙaddamar da binciken kisan tsohon janar a Abuja

Daga Buhari Aliyu Muhammad Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, ya bayar da umurnin gudanar da binciken kisan da wasu da ake zargi 'yan fashi ne suka yi wa wani tsohon Janar a gidansa da ke Abuja. Maharan sun kutsa gidan marigayin - Burgediya Janar Uwem Udokwere mai ritaya inda suka kashe shi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kashe tsohon janar ɗin a gidansa da ke rukunin gidajen 'Sunshine' a unguwar Lokogoma da ke birnin tarayyar, ranar Asabar da tsakar dare. Kwamishinan 'yan…
Read More
‘Yan fashi sun harbe wani tsohon soja a Abuja

‘Yan fashi sun harbe wani tsohon soja a Abuja

Wasu da ake zargin yan fashi ne, sun harbe wani tsohon soja, Birgediya janar Uwem Harold a cikin gidan sa da ke Abuja. Kwamishinan 'yan sandan Abuja cikin wata sanarwa, yace sun tura a fara bincike domin gano wanda sukai wannan aika aika. Bayan haka, kwamishinan ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma sake jaddada cewa hukumar yan sanda zatai iya bakin kokarin ta domin ganin ta cafko wanda sukai wannan mugun aiki.
Read More
Hukumomin samar da haraji na bin Gwamnatin Tarayya Tiriliyan N3, inji FAAC

Hukumomin samar da haraji na bin Gwamnatin Tarayya Tiriliyan N3, inji FAAC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Asusun Kasafin Kuɗin Nijeriya, FAAC, ya bayyyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta iya fuskantar asarar Naira Tiriliyan 2.97 da Dala Miliyan 36.33 idan hukumomin samar da kuɗaɗen shiga a ƙasar nan ba su daidaita kuɗaɗen shiga da aka tara ba. Adadin da wasu hukumomin da ba a bayyana sunayensu ke bin Gwamnatin Tarayya tun daga watan Afrilun 2024 an bayyana shi ne a lokacin taron kwamitin Asusun Kasafin Kuɗin Nijeriya. Mataimakin shugaban kwamitin da ya wakilci shugaban kwamitin Kabir Mashi a wajen taron ya ce, ana cigaba da ƙoƙarin sasantawa da hukumomin da abin ya shafa…
Read More
Masu kuɗi sun fi talaka cin dankalin Hausa saboda tsada – Tijjani Abdullahi

Masu kuɗi sun fi talaka cin dankalin Hausa saboda tsada – Tijjani Abdullahi

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD Masu kuɗi sun fi talaka cin dankalin Hausa, don na Turawa sai masu mulki a Babbarn Birnin Tarayya Abuja, saboda tsadarsa da kuma ƙarancinsa a wannan zamani. Alhaji Tijjani Abdullahi, wanda shine Shugaban Kasuwar masu sayar da kayan marmari na lambu a unguwar rukunin gidajen Zangon Daura da ke Birnin Tarayya Abuja, ne ya shaida wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, farashin dankalin Turawa ya yi tashin Gwauron Zabo daga Naira 4,000 zuwa 8,000 zuwa 16,000, wanda ya sa har masu kuɗi da dama dake Abuja suka guje masa, inda suka koma wa na Hausa wanda shi…
Read More

Za a fara cirar kuɗi da katin ɗan ƙasa a watan Agusta-NIMC

Daga Khadija Abubakar Hukumar kula da katin zama ɗan ƙasa (NIMC), ta ce nan da watanni biyu za ta inganta katin zama ɗan ƙasa ta yadda zai ke amfani guda uku ga masu shi. Wani jami'in hukumar da bai yadda a faɗi sunansa ba ya sanar manema labarai hakan a ranar Juma'a, inda ya ce kati zai fara amfani a matsayin shedar zama ɗan ƙasa, da ɓangaren cirar kuɗi kamar katin 'ATM' sannan da kuma wasu harkokin rayuwa. Ya ƙara da cewa, hukumar tana iya ƙoƙarinta wajen cimma hakan, domin kuwa a halin yanzu, ta fara gwajin yiwuwar haka, dan…
Read More

Kotu ta bada umurnin riƙo na din-din-din ga kadarorin naira biliyan 12 da ke da alaƙa da Emefiele

Daga Sadiq Muhammad Wata babbar kotun tarayya dake Jihar Legas, ta jaddada cewa, za a cigaba da riƙe kadarorin gwamnatin tarayya da aka ƙwace a hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele waɗanda adadinsu ya kai sama da naira biliyan goma sha biyu. Mai Shari'a Chukwujekwu Aneke, ya yi hukuncin biyo bayan da wani jami'in hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da laifukan da suka shafi kuɗi (EFCC), Chineye Okezie ya shigar da ƙara, inda ya ce a shari'ar karo na ƙarshe, za cigaba da riƙe kadarorin na din-din-din. A ranar 5 ga watan Yuni, 2024…
Read More

Rundunar Soji ta hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda a Kaduna

Daga Bala Muhammad Rundunar Sojin Najeriya, ta ce ta kashe wani sanannen ɗan ta'adda mai suna Kachalla Ragas tare da wasu gungun ƴan ta'adda a wani hari da ta kai a ƙaramar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna. Kwamishinan sa-ido kan aikin jami'an na ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar da sanarwar, inda ya ce jami'an sun kai harin ne ƙarƙashin atsayen 'Whiri Punch' wanda ya yi sanadiyar mutuwar ƴan bindigan da dama ciki har da manyan kwamandojinsu a yankin ƙauyen Bula dake dajin Yadi a ƙaramar hukumar. Yayin miƙa rahoton ga gwamnatin Jihar, Samuel ya ce…
Read More
Ta ƙona mahaifiyarta ‘yar shekara 86 kan zargin jefa ta a ƙangin talauci

Ta ƙona mahaifiyarta ‘yar shekara 86 kan zargin jefa ta a ƙangin talauci

Wata mata 'yar shekara 45 mai suna Abiodun ta banka wa mahaifiyarta ’yar shekara 86 wuta a garin Ondo da ke Ƙaramar Hukumar Ondo ta Yamma a Jihar Ondo. Abiodun, wadda aka fi sani da ‘Iya Sunday’ ta ce ta ƙona mahaifiyarta ne saboda zargin ta da zamowa silar wahalhalunta a rayuwa. Wani ganau mai suna Sola Oladele ya bayyana cewa wadda ake zargin ta zo gidan mahaifiyarta ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5 na safe ta kira ta kafin ta zuba mata man fetur sannan ya banka mata wuta. Ganau ɗin ya ce, matar da faɗa masa…
Read More

Ƴar Galadiman Dutse mai shekaru 62 ta rasu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Iyalan gidan Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammad Sanunsi na cikin alhini, biyo bayan rasuwar ɗaya daga cikin ƴaƴansu mai suna Hafsatu Basiru Sanusi. Marigayiyar wacce aka haifa a ranar 31 ga watan Mayu, 1962, ta bar ƴaƴa huɗu cikin har da Lukman Mahmoud Isa Dutse, ma'aikacin bankin CBN reshen Abuja, da kuma Alawiyyah Mahmoud Isa Dutse, ma'aikaciyar kamfanin inshora na ƙasa (NDIC) dake Abuja. Wasu daga cikin ƴan uwanta sun haɗa da; Jamilu Basiru Sanusi, Turakin Dutse da Zahraddeen Basiru Sanusi, Dan Isan Dutse, da kuma Sanusi Basiru Sanusi, Ɗan Darman Dutse. Hafsatu ta kasance jigo…
Read More
An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

An samu wata hatsaniya a yankin Ojurowo da ke bangaren Eko jihar Legas. Wata mata a ka kama da sata da sayar da ƙananan yara. Jaridar City Round ta rawaito cewa, matar ta saci yaran daga Ijora sannan ta kawo su Eko don ta sayar. A wani faifan video dake yawo a shafin sada zumunta na X, an ga mutane zagaye da wani gini da ake zargin nan wannan matar ke aiwatar da haramtaccen kasuwancin ta. Kamar yadda aka jiyo sautin wani a faifan bidiyon, yana cewa matar ta amsa cewa za ta siyar dasu a kan kuɗi naira 250,000.…
Read More