Labarai

Bankin Duniya ya tallafa wa manoman 620 a Nasarawa

Bankin Duniya ya tallafa wa manoman 620 a Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya fara rabon wani tallafin kuɗi wanda Bankin Duniya ya raba wa manoma 620 a juhar waɗanda aka zaƙulo su daga yankunan karkara 10 a faɗin jihar. Da yake jawabi a wajen rabon tallafin wanda aka gudanar a garin Doma, hedikwatar ƙaramar hukumar Doma a jihar, Gwamnan ya ce raba wa manoman kuɗaɗen yana daga cikin ƙudirin Gwamnatin Tarayya ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya na ci gaba da taimaka wa manoma a jihar don inganta fannin noma da zummar samun wadataccen abinci. Ya ce, ita ma gwamnatin sa…
Read More
Tinubu ya buƙaci gwamnonin Arewa ta tsakiya su kasance tsinsiya baɗaurinki guda DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Tinubu ya buƙaci gwamnonin Arewa ta tsakiya su kasance tsinsiya baɗaurinki guda DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙalubalanci masu ruwa da tsaki da duka mambobin jam’iyyarsu ta APC maici a yankin Arewa ta tsakiya a ƙasar nan su tabbatar sun ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Wannan kiran haɗin kai Shugaban Ƙasar ya yi ne a lokacin wani gagarumin taron masu ruwa-da-tsakin jam’iyyar APC ɗin a Arewa ta tsakiya wanda aka gudanar a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar Nasarawa. Shugaba Tinubu wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya wakilce shi a wajen taron, ya jaddada mahimmancin haɗin kai don cigaban jam’iyyar ta APC da ma ƙasa baki ɗaya. Ya…
Read More
CJN ya sammaci manyan alƙalan kotunan Kano kan ba da umarni masu karo da juna

CJN ya sammaci manyan alƙalan kotunan Kano kan ba da umarni masu karo da juna

Babban Alƙalin Ƙasa (CJN), Justice Olukayode Ariwoola, sammaci Babban Alƙalin Kotun Tarayya da takwaransa na Babban Kotun Jihar Kano, kan su zo don ya ji yadda aka yi suka bayar da umarni masu cin karo da juna game da dambarwar sarautar Kano wanda hakan ya haifar da rashin tabbas. Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali S. A. Amobeda, ta ba da umarnin fitar da Muhammadu Sanusi II daga Fadar Ƙofar Kudu, tare da buƙatar a mai da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, kan kujerar Sarkin Kano. A hannu guda, ita ma Babbar Kotun Jihar Kano…
Read More
Tinubu ya rattaɓa hannu kan tsohon Taken Ƙasa ya zama doka

Tinubu ya rattaɓa hannu kan tsohon Taken Ƙasa ya zama doka

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanya ya rattaɓa hannu kan Dokar Taken Ƙasa inda a yanzu za a koma amfani da tsohon taken ƙasa wanda Turawan mulkin mallaka suka samar. Tuni dai wannan al'amari ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan ƙasa. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman da Majalusar ta yi a ranar Laraba. Haka nan, Akoabio ya ce Shugaba Tinubu ba zai yi wa Majalisar jawabi ba illa iyaka ya ƙaddamar da sabon taken na Nijeriya. Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce Tinubu ya soke gabatar da jawabin ne kasancewar Ranar…
Read More
Gwamna Abba ya haramta zanga-zanga a faɗin Kano

Gwamna Abba ya haramta zanga-zanga a faɗin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusif, ta haramta shirya kowane nau'in zanga-zanga a faɗin jihar. Gwamna Abba ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar Laraba. Ya ce, ɗaukar wannan matakin ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu a kan cewa wasu maƙiya jihar sun shirya yin zanga-zangar nuna goyon baya ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero. Hakazalika, Gwamnan ya umarci dukkan hukumomin tsaron jihar da su tabbatar da kama dukkan waɗanda suka samu sun gudanar da…
Read More
MƊD ta yi alƙawarin tallafa wa Nijeriya kan shirin samar da mafita a Arewa rewa maso-Gabas da aka ƙaddamar

MƊD ta yi alƙawarin tallafa wa Nijeriya kan shirin samar da mafita a Arewa rewa maso-Gabas da aka ƙaddamar

A wani gagarumin yunƙuri na magance matsalar gudun hijira a Jihohin Borno, Adamawa, da Yobe na Nijeriya, Gwamnatin Nijeriya da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ƙaddamar da tsare-tsare na jihohi kan mafita mai ɗorewa don magance matsalar ‘yan gudun hijirar cikin gida. Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma Mai Ba Da Shawara na Musamman Kan Hanyoyin Magance Rarrabuwar Kawuna a Cikin Gida Robert Piper, yayin taron kaddamar da taron a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya ce; “Za mu tsaya a bayanku. "Bari in nanata kudurinmu a madadin Majalisar Ɗinkin Duniya: Za mu ci gaba da ba da…
Read More
Zargin cushen kasafi: Majalisa ta yi wa Sanata Abdul Ningi afuwa

Zargin cushen kasafi: Majalisa ta yi wa Sanata Abdul Ningi afuwa

Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata Abdul Ahmed Ningi afuwa tare da kiran sa ya koma bakin aiki bayan da ta dakatar da shi a ranar 12 ga watan Maris, 2024. A ranar Talata Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Sanata Abba Moro, ya gabatar da buƙata dawo da Ningi tare da yin dama a madadin Ningin kan abin da ya faru. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, shi ne ya ba da sanarwar dawo da Ningi bakin aiki bayan da wasu daga cikin sanatotcin suka ruƙi a yi masa afuwa. Afuwar na zuwa ne makonni biyu kafin ƙarewar wa'din dakatarwa…
Read More
Shekara ɗaya a kan mulki: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka a Bakura, Maradu

Shekara ɗaya a kan mulki: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka a Bakura, Maradu

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da muhimman ayyukan cigaban al'umma a yankunan ƙananan hukumomin Bakura da Maradun da ke shiyyar Zamfara ta yamma. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Lawal yake cika shekara ɗaya riƙe da ragamar mulkin jihar ta Zamfara. Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa, Gwamna Lawal ya kai ziyara ƙananan hukumomi guda uku da suka haɗa da: Mafara da Bakura da kuma Maradun. Ya ƙara da cewa, yayin ziyarar, Lawal ya nuna damuwa kan halin da ya tarar da Babban Asibitin Ƙaramar Hukumar Talatan Mafara saboda rashin ingnci. Sanarwar da…
Read More
SERAP ta sake maka gwamnonin jihohi 36 da ministan Abuja a kotu

SERAP ta sake maka gwamnonin jihohi 36 da ministan Abuja a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Fafutukar Yaƙi da Cin Hanci a Nijeriya, SERAP, ta kai ƙarar gwamnonin jihohin ƙasar 36 da Ministan Birnin Tarayya, Abuja, saboda zarginsu da gaza yin bayanin yadda suka kashe maqudan kuɗaɗen da suka samu daga kason Asusun Tarayya na FAAC, tun daga shekarar 1999. Cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare ya fitar ranar Lahadi, ya ce qungiyar ta ɗauki matakin ne sakamakon rahoton da ta samu cewa a cikin watan Maris FAAC ta raba Naira Tiriliyan 1.123 tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi. Ƙunhiyar ta ce, haka…
Read More
Abubuwan da suke nuna ka samu sana’a mai kyau – Likitan Sana’a

Abubuwan da suke nuna ka samu sana’a mai kyau – Likitan Sana’a

Daga AMINA YUSUF ALI A tattaunawarmu da Badamasi Aliyu Abdullahi wanda aka fi sani da likitan sana'a, wanda ƙwararre ne a kan sanin madafa da mafita a game da sana'o'i da dabarun bunƙasa tattalin arziki. Ya bayyana mana wasu hanyoyi da mai sana'a zai gane cewa sana'ar da yake ciki ko aikin da yake yi sana'a ce ko aiki ne mai kyau da ya dace da shi. A tattaunawar ga wasu dalilai da ya kawo. Idan kana shauƙin ta. Son sana'arka shi ne tubalin gina ta da yin haƙuri da juriya da kasuwanci ke buƙata. Idan ba soyayyar abinda ka…
Read More