Labarai

Yadda kotu ta dakatar da EFCC daga kama Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano ta fitar da takardar hana kama ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar NNPP a babban zaɓen shekarar 2023, Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai, wacce ke ƙunshe da hana kamawa ko cin mutunci ko kuma tsare su. Mutanen sun haɗa da Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Clement Anele, Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Mai Shari'a Yusuf Ubale Muhammad ya fitar da takardar dake ɗauke da bayanin wanda ya fara aiki daga ranar 5 ga watan yunin shekararnan. Kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar…
Read More
Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulkin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulkin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Wata ƙungiyar 'yan majalisar wakilai 35 ta gabatar da ƙudurin wa'adin mulki na shekaru shida ga Shugaban ƙasar Najeriya da ma gwamnonin jihohi.'Yan majalisar sun kuma ya ce ya kamata a riƙa gudanar da zaɓukan muƙaman siyasa a rana guda, don kuɓutar da ƙasar daga kashe maƙudan kudaɗe wajen gudanar da zaɓe.Mai magana da yawun ƙungiyar, Hon., Ikenga Imo Ugochinyere, wanda ya jagoranci sauran mambobin ƙungiyar, ya bayyana shida daga cikin ƙudurin doka hamsin, wanda wasu daga cikinsu sun riga sun tsallake karatun farko, a yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin.
Read More
Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take.

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Kungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ƙasa, ta ƙauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Kano, nan take. Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar Aminu Ahmed Getso ya sanyawa hannu a litinin din nan. Getso ya bayyana kyara, cin mutunci da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu a fadin jihar. Kazalika ƙungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da waɗanda ba yan yaridu ba wajen ɗaukar harkokin gwamnati, maimakon barin yan jaridu su yi aikinsu bisa ƙwarewa. A saboda haka ne ƙungiyar…
Read More

Mafi ƙarancin albashi: Yayin da ake ƙarƙare batun a ranar Litinin, gwamnati ta gabatar da naira 62,000 ga NLC da masu ruwa da tsaki

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A yau Litinin ne ake sa ran kammala batun ƙayyade mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Najeriya, yayin da ƙungiyoyin ƙwado ke sauraron amsar tayin naira 250,000 daga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta yi. Shuwagabannin ƙungiyoyin ƙwado na ƙasa sun bada wa'adin 10 ga watan yuni a matsayin ranar ƙarshe da zasu saurari amsar gwamnatin tarayya game da batun. A ranar Jumma'ar da ta gabata ne kwamitin ƙayyade ƙarancin albashi ta ƙasa ta gudanar da wani zama, inda aka cimma yarjejeniyar naira dubu 62 tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da kuma na haɗaɗɗiyar kungiyar ma'aikatu masu…
Read More
Mata da yawa ba sa kai tunaninsu kan yadda za su taimaki mazansu a sana’arsu – Halima Ahmad Ɗahir

Mata da yawa ba sa kai tunaninsu kan yadda za su taimaki mazansu a sana’arsu – Halima Ahmad Ɗahir

A yau dai shafin Gimbiya ya ɗauko wa masu karatu wadda ta cancanci mata su kira ta da gimbiya, kasancewar ta jajirtacciyar mace kuma abin koyi ga mata. Mai karatu zai amince da hakan ne ta irin nasarorin da ta samu a ɓangarorin da mata da yawa suke ganin mata ba sa samun kai. Jajirtacciyar 'yar jarida ce da ta kai matsayin riƙe babban matsayi a aikin jarida, kuma ta kwashe tsayin shekaru ashirin da takwas a cikin sa. Baya ga haka, ta zama abin koyi ga mata ta ɓangaren zamantakewar aure, inda yanayin irin nata zaman aure kawai zai…
Read More
‘Yan bindiga na samun bayanai fiye da yadda muke samu – Dikko Raɗɗa

‘Yan bindiga na samun bayanai fiye da yadda muke samu – Dikko Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya ce a halin yanzu 'yan bindiga na samun bayanan sirri fiye da yadda gwamnati ke samu lamarin dake ƙara dagula ƙoƙarin jami'an tsaro na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar. "Suna samun bayanai fiye da yadda muke samu". Inji shi. Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron gaggawa kan matsalar tsaro wanda ya jagoranta tare da sauran jami'an tsaro dake jihar. A cewarsa, "Makahon yaƙi ne ake yi da 'yan bindiga saboda ba ka sanin waye maƙiyinka ko masoyinka saboda wani lokaci duk da masu ba…
Read More
Tinubu ya sa zamowar Osimhen Gwarzon Afirka a nasarorinsa na shekara guda

Tinubu ya sa zamowar Osimhen Gwarzon Afirka a nasarorinsa na shekara guda

Daga MAHDI M. MUH'D Tinubu ya saka nasarar da Osimhen ya samu na zama gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a cikin nasarorin da ya samu yayin da ya cika shekara guda a kan karagar mulki. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya ɗan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika na bana a matsayin wani ɓangare na nasarorin da ya samu yayin da ya cika shekara guda a kan karagar mulki. Idan za a iya tunawa, Osimhen ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika na 2023 bayan ya doke Mohamed Salah da sauran su, inda…
Read More
NAWOJ ta taya Raɗɗa murnar cika shekara ɗaya kan karagar mulki

NAWOJ ta taya Raɗɗa murnar cika shekara ɗaya kan karagar mulki

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙungiyar Mata ‘yan Jarida ta Nijeriya (NAWOJ), reshen jihar Katsina, ta miƙa saƙon taya murna ga Gwamna Dikko Umar Raɗɗa bisa cikar sa shekara guda kan karagar mulki. Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabar ƙungiyar, Hannatu Mohammed da kuma sakatariyar ƙungiyar, Faith Awa Maji. NAWOJ ta yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar, musamman wajen bai wa mata ƙarfin gwiwa wajen ganin sun cimma burinsu. Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mai Girma Gwamna, wa’adin mulkinka ya samar da kyakkyawan yanayin…
Read More
Sojojin Nijar sun damƙe ƙasurgumin ɗan bindigar Nijeriya, Kachalla Ɓaleri

Sojojin Nijar sun damƙe ƙasurgumin ɗan bindigar Nijeriya, Kachalla Ɓaleri

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɓaleri, wanda tun da farko ya tsere daga hannun sojojin Jamhuriyar Nijar, da ake kira 'Operation Farautar Bushiya,' sun kama shi a ranar Talata a unguwar Rouga Kowa Gwani da ke garin Guidan Roumdji. Da yake tabbatar da kamun ɗan bindigar, Babban Hafsan Rundunar Operation Faraoutar Bushiya, Kanar Mohamed Niandou, ya ce an kawo ƙarshen mulkin Ɓaleri a ranar Talata yayin da yake ganawa da mutanensa domin shirya kai hare-hare a Nijeriya da Nijar. “Gwamnan yankin, CGP Issoufou Mamane, da mai shigar da ƙara na ƙasar, Adamou Abdou Adam, sun yaba da ƙwarewa da jajircewar…
Read More
NOA ta bai wa jami’anta sa’o’i 72 su haddace sabon taken ƙasa

NOA ta bai wa jami’anta sa’o’i 72 su haddace sabon taken ƙasa

Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), ta bai wa jami'anta da ke ƙananan hukumomi 774 da ake da su a Nijeriya umarni a kan su haddace sabon taken ƙasa a tsakanin sa'o'i 72, wato ya zuwa 3 ga watan Yuni. Ta ce jami'anta da ke yankunan karkara su ne su tabbatar da ɗabbaƙa sabon taken ƙasar daga tushen al'umma. Kazalika, hukumar ta ce, "muna aiki tare da Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) wajen tabbatar da makarantun faɗin ƙasar nan sun fara amfani da sabon taken na ƙasa." Cikin sanarwar da hukumar ta fitar, an jiwo Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai,…
Read More