Labarai

Gwamnatin Kaduna za ta tallafi manoman citta a jihar

Gwamnatin Kaduna za ta tallafi manoman citta a jihar

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Kaduna tare da hukamar gwamnatin Tarayya za su tallafa wa manoman citta da suka tafka hasara a kakar bara Gwamnatin Kaduna tare da hukamar gwamnatin Tarayya za su tallafa wa manoman citta da suka tafka hasara a kakar baraBiyo bayan ibtila’in da ya afka wa manoman Citta da ya yi sanadiyyar tafka gagarumar asara a kakar noman bara da wasu manoman suka rasa ilahirin amfanin gonarsu, jin ƙai da tallafi na tafe cikin gaggawa daga mahukunta daga Kaduna da gwamnatin Tarayya. Asusun tallafa wa manoma na gwamnatin tarayya NADF da hukumar…
Read More
Ana sa ran ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su janye ficewa daga ECOWAS – Ndume

Ana sa ran ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar za su janye ficewa daga ECOWAS – Ndume

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni dai sun bayyana cewa, ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na shirin janye matakinsu na ficewa daga ƙungiyar Ecowas mai raya tattalin arzikin qƙasashen Afirka ta Yamma. Sanata Ali Ndume - wanda ɗan majalisar ƙungiyar Ecowas ɗin ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Kano, a yayin da majalisar ƙungiyar ke ci gaba da gudanar da taronta a jihar. Dan majalisar ya ce an cimma duk wani abu da ake buƙata domin maido da ƙasashen cikin ƙungiyar ta Ecowas. "An riga an warware saɓanin da ya kai ga ɗaukar matakin fita daga…
Read More
Mafi ƙarancin albashi: NLC ta ƙara matsa lamba a kan gwamnatin Tarayya

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta ƙara matsa lamba a kan gwamnatin Tarayya

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyoyin 'yan ƙwadago ta NLC da TUC sun nemi gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta biya Naira 497,000 maimakon Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi. A taqaice dai ma wato sun sassauta abin da suke buƙata gwamnati ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar zuwa naira 497,000. A baya dai ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce dage a kan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da suke son gwamnatin ƙasar ta amince da shi. Yayin cigaba da tattaunawar a ranar Talatar da ta gabata, ƙungiyoyin sun kuma yi watsi da sabon ƙudirin da gwamnati…
Read More
Kotu ta ba wa ‘yan sandan Kano umarnin fitar da Aminu Ado daga Gidan Sarki na Nasarawa

Kotu ta ba wa ‘yan sandan Kano umarnin fitar da Aminu Ado daga Gidan Sarki na Nasarawa

Babbar Kotu a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali Amina Adamu Aliyu, ta bai wa Kwamishinan 'Yan Sandan Kano umarni a kan su gaggauta fitar da Aminu Bayero daga Fadar Sarkin Nasarawa inda yake da zama a halin yanzu. Haka nan, Kotun ta ba da umarnin haramta wa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗun da aka tuɓe, ɗaukar kansu a matsayin sarakai har sai ta surari ƙarar da ke gabanta. Sauran da hanin ya shafa su ne tuɓaɓɓun sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye. Wannan umarni ya biyo bayan ƙararar da lauyan mai ƙara, Ibrahim Isa…
Read More
Za a yi wa yara 6000 gwajin cutar Tarin Fuka a Kano — Dr Labaran

Za a yi wa yara 6000 gwajin cutar Tarin Fuka a Kano — Dr Labaran

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da yin aiki tukuru wajen ganin an kawar da cutar Tarin Fuka (TB) a jihar, Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Litinin, a wani ɓangare na tunawa da ranar gwajin tarin TB na duniya da yake gudana a duk ranar 27-5-2024. Dakta ya ce, za a yi sati guda ana aiwatar da wannan gwaje-gwaje, wanda baya ga gwajin cutar Tarin Fuka za a kuma yi gwajin cutar ƙanjamau da cutar cutar yunwa (Tamowa)…
Read More
Gwamnati ta dakatar da jirgin Air Nigeria har sai baba-ta-gani

Gwamnati ta dakatar da jirgin Air Nigeria har sai baba-ta-gani

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar cewa, ta dakatar da aikin kamfanin jirgin saman Nijeriya, wato Air Nigeria. Sanarwar wadda aka fitar a ranar Litinin ta ce, dakatarwar ta har baba-ta-gani ce. Ministan Sufurin Jirgin Sama, Festus Keyamo, shi ne ya bayyana haka yayin da yake ba da bayani kan ayyukan ma'aikatarsa a matsayin ɓangare na cika Shuga Bola Tinubu shekara guda a ofis. Da yake ƙarin haske kan dalilin dakatarwar, Keyamo ya ce, jirgin da aka nuna cewa ta Nijeriya ne ba gaskiya, rufa-rufa ce kawai aka yi wa lyan ƙasa a wancan lokaci.
Read More
Kotu ta tabbatar da nasarar da Ododo, Diri suka samu a zaɓukan Kogi da Bayelsa

Kotu ta tabbatar da nasarar da Ododo, Diri suka samu a zaɓukan Kogi da Bayelsa

Kotun Sauraren Ƙararrakin Gwamna a Jihar Kogi mai zamanta a Abuja, ta tabbatar da nasarar da Usman Ododo na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jiharda ya gudana a ranar 11 ga Nuwamban 2023. Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ado Birnin-Kudu, ƙarar da aka shigar kan nasarar da Ododo ya samu ba ta da tushe, a don haka aka yi watsi da ita. Kazalika, Kotun ta ce masu ƙarar, Jam'iyyar SDP da ɗan takararta Murtala Ajaka, zun gaza kare zargin da suke yi da hujjoji masu gamsarwa. A wata mai kama da wannan, Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan…
Read More
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya gamu da cikas sa’a guda da fara aiki

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya gamu da cikas sa’a guda da fara aiki

A ranar Lahadi Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya gamu tsaiko a hanya a yankin Jere, Kaduna, sa’a guda da fara aiki. Jirgin mai dauke da gomman fasinjoji, ya baro Kaduna ne da misalin karfe 8:05 na safe da nufin zuwa Abuja inda ya gamu da cikas. Bayanai sun ce kafafuwan uku daga cikin taragon jirgin ne suka sauka a layi wanda hakan ya tilasta wa jirgin tsayawa. An ga jami’an tsaro daban-daban a wurin da lamarin ya faru don bai wa jama’a kariya. Hukumar Binciken Tabbatar da Kariya ta Nijeriya (NSIB) ta ce ta tura jami’anta yankin domin gudanar…
Read More
Hajjin Bana: Ɗaya daga cikin alhazan Nijeriya ya rasu a Makka

Hajjin Bana: Ɗaya daga cikin alhazan Nijeriya ya rasu a Makka

Rahotanni daga birnin Saudiyya sun ce, Allah Ya yi wa wani alhajin Najeriya, Alh. Muhammad Suleman rasuwa a Makka a ranar Lahadi. Majiyarmu ta ce marigayin wanda dan asalin Jihar Kebbi ne daga yankin Karamar Hukumar  Argungu, ya rasu ne sakamakon fama da rashin lafiya. Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Kebbi, Faruku Aliyu-Enabo, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema Larabai a Makka. “Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da rashin lafiya, kuma an sallaci gawar a Masallacin Harami (Ka’aba), kana aka binne shi daidai da karantarwar Islama,” in ji Faruk. Jami’in ya yi amfani…
Read More
Sarkin Musulmi ya ƙaddamar da Cibiyar Ilimin Al-Ƙur’ani ta tsangaya a Zamfara

Sarkin Musulmi ya ƙaddamar da Cibiyar Ilimin Al-Ƙur’ani ta tsangaya a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a  Gusau Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alh Sa'ad Abubakar III ya kaddamar da cibiyar koyar da Al-Kur'ani ta jihar Zamfara a ranar Lahadi a garin Gummi, hedikwatar karamar hukumar Gummi ta jihar. Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya wa cibiyar sunan Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III cibiyar ilimin Kur'ani mai tsarki. Da yake jawabi a lokacin kaddamar da aikin, Sultan Sa’ad Abubakar ya yaba wa Gwamnatin Zamfara bisa wannan sabuwar dabara. A cewarsa, cibiyar za ta magance barace-barace a tsakanin almajirai da Kuma bai wa almajiran makarantun allo samun damar yin ilimin boko. Basaraken…
Read More