06
Sep
Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da yiwuwar ƙarin kuɗin kujerar Hajji a yayin Hajjin 2024 idan Allah Ya kai mu. Hukumar ta ce Naira miliyan 4.5 shi ne mafi ƙarancin kuɗin da maniyyaci zai iya sakawa a asusun ajiya a ƙarƙashin hukumar wanda hakan ke nuni za a fuskanci ƙarin kuɗin kujerar Hajji a 2024. NAHCON ta ce ya zuwa yanzu tana nazarin rahotannin da kwamitoci suka gabatar mata dangane da Hajjin 2023 da ya gabata. Da yake jawabi a wajen taron manema labarai da hukumar ta shirya a Abuja, shugaban NAHCON na ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan, ya…
