Labarai

Rikicin Boko Haram ya yi ajalin mutum 35,000 a Arewa maso Gabas – MƊD

Rikicin Boko Haram ya yi ajalin mutum 35,000 a Arewa maso Gabas – MƊD

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ce kimanin mutum 35,000 ne suka mutu tun fara rikicin Boko Haram daga shekara ta 2009 zuwa watan Agustan 2023. Shugaban ofishin hukumar a Jihar Adamawa, Elsie Mills-Tetty ce ta bayyana hakan yayin wani taron horar da sojoji a kan kare haƙƙin bil Adama da kuma kare fararen hula a Yola ranar Laraba. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa hukumar ta shirya taron ne domin ba su horo kan hanyoyin kiyaye haqqoqin jama’a yayin ayyukansu. Elsie, wacce wani jami’i…
Read More
Nasarorin da matar Gwamnan Kebbi ta samu cikin kwana 100 a ofis 

Nasarorin da matar Gwamnan Kebbi ta samu cikin kwana 100 a ofis 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Hajiya Zainab Nasir Idris (Nasare) matar Gwamnan Jihar Kebbi, wacce ake wa kirari da mace mai kamar maza da ke da burin canza rayuwar mabuƙata zuwa mawadata ta hanyar bayar da tallafi a inda ya dace. Kasancewar ta matar gwamna, hakan bai hana ta ayyukan da ta taso tana aiwatarwa ba kafin yanzu.   A cikin kwanaki 100 da ta yi na matar gwaman, Hajiya Nasare ta sami nasarar canza rayuwar mutane da yawa, musamman mabuƙata a faɗin jihar ta Kebbi, inda ta ba wa waɗansu damar kaiwa ga wani bagire da a baya ba…
Read More
Kamfanin Google ya naɗa ɗan Nijeriya muƙamin Mananjan Darakta na Afirka 

Kamfanin Google ya naɗa ɗan Nijeriya muƙamin Mananjan Darakta na Afirka 

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne dai kamfanin Google ya ba da sanarwar naɗin wani ɗan Nijeriya, Alex Okosi a matsayin Manajan Darakatan Google na Afirka domin taimaka wa kasuwanci da tattalin arziki su bunƙasa.  Mataimakin Shugaban EMEA na Google, Meir Brand shi ya hayyana hakan a wani jawabi. Sannan ya ce, a yanzu Mista Okosi shi ne zai ja ragamar ayyukan Google a Afirka. Mista Brand ya ƙara da cewa, wannan muƙami kuma zai taimaka wa biliyoyin masu amfani da shafin na Google su samu ƙarin abubuwa daga gare shi.   “Alex shugaba ne na…
Read More
An tsinci gawar ɗaliba cikin rami bayan vatarta

An tsinci gawar ɗaliba cikin rami bayan vatarta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An tsinci gawar wata ɗalibar Jami’ar Tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah, kwanaki biyu bayan ta ɓata. A cewar rahotanni, Deborah, wacce ɗaliba ce a sashen karatun aikin jinya, stream A, Faculty of Basic Medical Science, ta ɓata bayan ta tafi karatun daren Litinin, 4 ga Satumba, 2023. Abokan zamanta sun bayyana ɓatarta lokacin da ba ta dawo daga karatun dare ba. An tsinci gawar ta binne a wani rami mara zurfi a bayan jami’ar ba tare da idanunta ba a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba. Da ya ke mayar da martani kan…
Read More
Tinubu ya caccaki Obasanjo kan batun matatar man Fatakwal

Tinubu ya caccaki Obasanjo kan batun matatar man Fatakwal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan kalaman da ya yi kan matatar mai da ke garin Fatakwal na Jihar Ribas. A wata hira da ya yi da manema labarai kwanan nan, Obasanjo ya jaddada cewa,  matatun man ƙasar ba za su taɓa yin aiki yadda ya kamata ba matuqar sun ci gaba da zama a ƙarƙashin gwamnati. “Wani ya gaya min cewa Tinubu ya ce matatun man za su yi aiki a watan Disamba. Na ce wa mutumin matatun man ba za su yi aiki ba. Wannan ya samo…
Read More
Yadda aka yi jana’izar Sheikh Giro Argungu a Kebbi

Yadda aka yi jana’izar Sheikh Giro Argungu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi   An yi jana’izar shahararren malamin addinin Islama ɗin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu, a mahaifarsa ta Argungu da ke Jihar Kebbi. Shehin malamin ya rasu ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC)  dake garin Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, bayan gajeriyar jinya. Kafin rasuwarsa shi ne Babban Sakataren Tsare-tsare na Ƙungiyar Izala ƙarƙashin jagoranacin Sheikh Bala Lau dake da sharkwata a Kaduna. Malam Giro ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa addinin Musulunci da ya yi sanadiyyar ɗaruruwan mutane karvar addinin Musulunci ciki da wajen Nijeriya. Malam Giro ya rasu ne yana da shekaru 61, inda…
Read More
Raɗɗa ya taya Tinubu murnar samun nasara a kotu

Raɗɗa ya taya Tinubu murnar samun nasara a kotu

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya taya Shugaban Ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu murna dangane da nasarar da ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, inda kotun ta tabbatar da nasarar zaɓen da aka yi wa Shugaba Tinubu tare da korar ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour Party suka shigar, inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar farkon shekarar nan. Raɗɗa ya bayyana cewar hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da zaɓen da 'yan ƙasar nan suka yi wa…
Read More
Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Allah Ya yi wa fitaccen malamin Islam na ƙungiyar JIBWIS, Sheikh Abubakar Giro Argungu, rasuwa. A ranar Laraba Allah Ya yi masa cikawa a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan fama da rashin lafiya. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 68. Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya ba da sanarwar marigayin a shafinsa na Facebook a ranar Laraba. A na sa ran gabatar da jana'izar marigayin a wannan Alhamis kamar yadda Sheikh Bala Lau ya sanar.
Read More
Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa: Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotu

Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa: Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotu

Jam'iyyar Labour Party ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa kan ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata a watan Fabrairu, 2023. Cikin sanarwar da ta fitar bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Obiora Ifoh, ya ce ba a yi wa LP adalci ba kan ƙarar da ta shigar kan jam'iyyar APC da Tinubu. Ya ce jam'iyyar tasu za ta ɗauki mataki na gaba bayan tuntuɓar lauyoyinta bayan kuma ta amshi takardar shaidar hukuncin da kotun ta…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya yi zagayen duba aiki

Gwamna Dauda Lawal ya yi zagayen duba aiki

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kai ziyarar gani da ido a aikin hanyoyi da ake yi a Gusau, Babban Birnin Jihar. Aikin yana daga wani ɓangare na shirin bunƙasa birni da gwamnatin ta kawo, wanda kuma aka fara shi watan da ya gabata. Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnan ya bayyana farin ciki da yanayin da aikin ke tafiya. Ya ƙara da cewa, a yayin ziyarar duba aikin hanyar, dandazon jama’a ne suka yi wa gwamnan tarba ta musamman. Ya ce: “A ranar 18 ga watan Agustan…
Read More