Labarai

Abin da maigidanki ya shuka kika girba, ra’ayin ‘yan Nijeriya kan urwagidan Gwamnan Bauchi

Abin da maigidanki ya shuka kika girba, ra’ayin ‘yan Nijeriya kan urwagidan Gwamnan Bauchi

'Yan Nijeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu a soshiyal midiya dangane da halin da uwargidan Gwamnan Bauchi, Hajiya Aisha Bala Mohammad, da tawagrata suka tsinci kansu a lokacin da ta kai ziyara yankin Jamdan don ƙaddamar da cibiyar kula da lafiya. Hotunan da suka karaɗe kafafen sada zumunta na zamani sun nuna yadda Aisha Bala da tawagarta suka sha fama a hanya saboda rashin kyawun hanyar zuwa garin da suka kai ziyarar. Lamarin da ya kai matar Gwamnan ta sauka a motarta ta taka da ƙafafunta saboda matsalar caɓi a hanyar. Tuni dai wasu 'yan Nijeriya suka yi ra'ayin…
Read More
Biden ya jinjina wa Tinubu kan kare martabar dimokuraɗiyya

Biden ya jinjina wa Tinubu kan kare martabar dimokuraɗiyya

Shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka, ya yaba da shugabancin da Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ke yi wa ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS). Biden ya jinjina wa Tinubun ne la'akari da ƙoƙarin da ke ECOWAS ke yi wajen maido da tsarin mulkin dimokraɗiyya a ƙasar Nijar. Biden ya ce jajircewar da Tinubu ke yi wajen kare tsarin dimokuraɗiyya a Nijar da ma yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya abin a yaba ne. Ya byyana haka ne yayin ganawarsu da Tinubu a wajen taron G20 da ya gudana a Delhi, Kasar Indiya. Cikin sanarwar da ta fitar…
Read More
Kotu ta ƙwace kujerar ɗan majalisa daga hannun NNPP ta bai wa APC a Kano

Kotu ta ƙwace kujerar ɗan majalisa daga hannun NNPP ta bai wa APC a Kano

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a Jihar Kano ta tsige Yusuf Umar Datti na Jam'iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a jihar. Bayan tsige Datti daga kujerar ɗan majalisa tmda ta yi, kotun ta ayya abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso, a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta kama Datti da laifin ƙin ajiye aikin gwamnati a tsakanin kwana 30 kafin shiga zaɓe kamara yadda doka ta tanada. Kafin shiga zaɓen, ɗan siyasar ma'aikaci ne a Jami'ar Bayero ta Kano. Kazalika, Alƙali Azingbe ya ce…
Read More
Gwamnatin Buhari ta ɗaiɗaita tattalin arzikin Nijeriya – Khalifa Sanusi

Gwamnatin Buhari ta ɗaiɗaita tattalin arzikin Nijeriya – Khalifa Sanusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya ce tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gurgunta tattalin arziki ba tare da neman shawarar ƙwararru ba. Sarki Sanusi wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana hakan a wani saƙon bidiyo da ya aike wa ‘yan Nijeriya ta yanar gizo. Ya bayyana cewa wasu sun ribaci riƙon sakainar kashi da aka yi wa tattalin arzikin da har aka samu “wani yaro mara ilimi” ya mallaki jirgin sama a ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe. Ya buqaci ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri…
Read More
Tallafin man fetur na kowane ɗan ƙasa ne, cewar Gwamna Sule

Tallafin man fetur na kowane ɗan ƙasa ne, cewar Gwamna Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya gargaɗi waɗanda ke rabon kayayyakin tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar ta Nasarawa su tabbatar suna nuna gaskiya da riƙon amana su kuma guji son kai da sauran su ayayin da suke raba tallafin ga al’ummar jihar baki daya ko su fuskanci fushin gwamnatinsa. Gwamnan ya yi gargaɗin ne a lokacin da ake bikin ƙaddamar da rabon kayayyakin abinci na tallafin man a ƙaramar hukumar Karu a jihar ranar Laraba na mako da ake ciki 6 ga watan Satumbar shekarar 2023. Ya ce…
Read More
Dalilin da ya sa na zaɓi Yar’Adua a matsayin magajina – Obasanjo

Dalilin da ya sa na zaɓi Yar’Adua a matsayin magajina – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa ya zaɓi tsohon shugaban qasa, Marigayi Alhaji Umar Musa ‘Yar’Adua a matsayin magajinsa duk da ya san cewa ba shi da lafiya. Tsohon shugaban ƙasar a wata hira da ya yi da jaridar Yanar Gizo mai suna “TheCable” ya musanta zargin da ake masa na cewa da gangan ya sanya ’yan takara masu rauni don son kai. A cewarsa, ya ɗauki matakin ne saboda shawarwarin likitoci sun nuna cewa ‘Yar’Adua, wanda aka yi masa dashen ƙoda, ya cancanci zama Shugaban Ƙasa.…
Read More
Jami’ar Azman Kano za ta fara yin digiri a ɓangaren tuƙin jirgin sama

Jami’ar Azman Kano za ta fara yin digiri a ɓangaren tuƙin jirgin sama

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami'ar nan mai zaman kanta mai suna Azman University da ke Kano, za ta fara yin digiri a fannin koyon tuƙin jirgin sama wanda ya ke shi ne na farko a Nijeriya da ma Afirka ta Yamma. A zantawarta da manema labarai da ya gudana a harabar makarantar da ke 'Yargaya da ke kan titin Wudil ranar Talata, Shugabar Jami'ar Farfesa Fatima Batulu Muktar ta bayyana cewa Jami'ar Azman ta samu sahalewar yin kwasa-kwasan tuqin jirgin sama guda biyu da suka haɗa da; Aviation Management da kuma Aviation Security. Ta kuma ce Jami'ar Azman za…
Read More
Sanata ya ɗauki nauyin koyar da matasa da mata sama da 1000 sana’o’i a Kebbi

Sanata ya ɗauki nauyin koyar da matasa da mata sama da 1000 sana’o’i a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi A cikin wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa da kuma Hukumar Yawon Buɗe Ido (National Institute for Hospitality and Tourism da kuma Muhasaf Global Resources Ltd ) ya ɗauki nauyin koyar da matasa da mata sama da dubu ɗaya sana'o'in hannu a faɗin mazaɓarsa. Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da koyon sana'o'in Alhaji Sama'ila Ɗantagago a madadin Sanata Yahaya Abubakar ya bayyana cewa koyon sana'o'i ya zama wajibi ga kowane mutum don kare mutuncinsa da na iyalansa, da zarar mutum ba ya…
Read More
INEC ta karrama Sa’idu Bappah da mutum biyar a Gombe

INEC ta karrama Sa’idu Bappah da mutum biyar a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC a Jihar Gombe ta karrama Shugaban Sashin Injiniyoyi na hukumar Injiniya Sa'idu Bappa Yaya da wasu ma'aikata mutum 5 bisa jajircewar su a aiki a Jihar Gombe. INEC ta karrama ma'aikatan na ta ne bisa hazaƙar a aiki kafin zaɓe da bayan babban zaven shekarar 2023 da ya gabata. A jawabinsa a wajen taron karramawar da ya gudana a helkwatar hukumar Kwamishinan Zaɓen na Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Umar, yaba wa ma'aikatan ya yi bisa ƙwazon da suka nuna a aikin su wanda hakan ne sanadiyyar…
Read More
Shugaban ƙaramar Hukumar Koko a Kebbi ya bai wa ‘yan sanda sabbin motoci

Shugaban ƙaramar Hukumar Koko a Kebbi ya bai wa ‘yan sanda sabbin motoci

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulki ta Koko/Besse da ke Jihar Kebbi Honarabul Yahaya Bello Koko ya bai wa ofishin hukumar 'yan sanda motoci biyu ƙirar Peogeot 406 tare da gyara Hilux da ta lalace a ƙaramar hukumar. Honarabul Bello ya bayyana cewa ya lura da yadda jami'an 'yan sandan ke wahala bisa ga rashin abin hawa sanadiyyar lalacewar motar da su ke amfani da ita ƙirar Hilux da su ke sintiri da aikin ofis da ita duk da irin matsalar tsaro da ke barazana a wannan yankin. Ya ce ya zama wajibi a haɗa hannu da…
Read More