Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan kalaman da ya yi kan matatar mai da ke garin Fatakwal na Jihar Ribas.
A wata hira da ya yi da manema labarai kwanan nan, Obasanjo ya jaddada cewa, matatun man ƙasar ba za su taɓa yin aiki yadda ya kamata ba matuqar sun ci gaba da zama a ƙarƙashin gwamnati.
“Wani ya gaya min cewa Tinubu ya ce matatun man za su yi aiki a watan Disamba. Na ce wa mutumin matatun man ba za su yi aiki ba. Wannan ya samo asali ne daga bayanan da na samu daga Shell lokacin da nake shugaban ƙasa,” inji shi.
Amma da yake mayar da martani ta bakin Tope Ajayi, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Tinubu ya ce Obasanjo ba injiniya ba ne, don haka bai kamata ya yi irin waɗannan kalamai ba.
“Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, tare da girmama shi ba injiniya ba ne. Ba shi ne injiniyan da ke aiki a matatun man ba.
Don haka Injiniyoyi da Kamfanin NNPC sun ba shugaban qasa rahoto kuma sun ce zai yi aiki a watan Disambar bana,” ya faɗi haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho mai taken, ‘kwanaki 100 na mulkin Shugaba Tinubu’.
“Har yanzu muna da saura watanni huɗu. Zan ce tare da girmama tsohon shugaban ƙasa, wanda dattijo ne kuma ubanmu, abin da ya faɗa ra’ayinsa ne. Na gwammace in dogara da injiniyoyin da ke aiki a matatar. Don haka, ina ganin ya kamata mu jira har zuwa Disamba.”
A watan Agusta, Shugaba Tinubu ya ce matatar mai da ke Fatakwal za ta fara aiki a watan Disamba na 2023 bayan kammala kwangilar gyaran da ake yi tsakanin Kamfanin Mai na Nigeria National Petroleum Company Limited (NNPCL) da Kamfanin Maire Tecnimont SpA na Italiya.
Tayar da matatar man, idan aka kammala kamar yadda Tinubu ya yi alƙawari, zai rage dogaron Nijeriya kan shigo da mai da kuma dogaro da matatun ƙasashen waje.
Kamfanin na NNPC ya ce, ya na ƙoƙarin gyara matatun man da aka rufe gaba ɗaya a shekarar 2021 kuma ba a samar da ɗanyen mai ko kaɗan a cikin shekaru goma da suka gabata.