Yadda aka yi jana’izar Sheikh Giro Argungu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 
  
An yi jana’izar shahararren malamin addinin Islama ɗin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu, a mahaifarsa ta Argungu da ke Jihar Kebbi.

Shehin malamin ya rasu ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC)  dake garin Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, bayan gajeriyar jinya.

Kafin rasuwarsa shi ne Babban Sakataren Tsare-tsare na Ƙungiyar Izala ƙarƙashin jagoranacin Sheikh Bala Lau dake da sharkwata a Kaduna.

Malam Giro ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa addinin Musulunci da ya yi sanadiyyar ɗaruruwan mutane karvar addinin Musulunci ciki da wajen Nijeriya.

Malam Giro ya rasu ne yana da shekaru 61, inda ya bar mata huɗu da ’ya’ya da jikoki da dama. 

Tuni an yi jana’izarsa a garin Argungu jiya, Alhamis, kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.

Jana’izar dai ta sami halartar wakilan Fadar Shugaban Ƙasa, majalisun Dattawa da Wakilai, gwamnonin jihohin Kebbi, Malam Nasir Idris; Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu da na Zamfara Lauwali Dauda tare da ’yan majalisunsu.

Haka nan akwai Sanata Aliyu Wamakko; Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera da ’yan majalisarsa, manyan malaman addini, wakilan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ’yan siysa, ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamanti daga Nijeriya, Nijar, Burkina Faso, Togo, Ghana  da sauran ƙasashen Afrirka.

Malam Nasiru Abubakar Mera Mera, Gwamnatoci da al’ummar Musulmi daga ko’ina a faɗin duniya sun cigaba da nuna jimami tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsu bisa wannan gagarumin rashi.

Mu na yin addu’ar Allah ya gafarta masa, ya karɓi ibadarsa kuma ya yafe kurakurensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *