Gwamna Dauda Lawal ya yi zagayen duba aiki

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kai ziyarar gani da ido a aikin hanyoyi da ake yi a Gusau, Babban Birnin Jihar.

Aikin yana daga wani ɓangare na shirin bunƙasa birni da gwamnatin ta kawo, wanda kuma aka fara shi watan da ya gabata.

Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnan ya bayyana farin ciki da yanayin da aikin ke tafiya.

Ya ƙara da cewa, a yayin ziyarar duba aikin hanyar, dandazon jama’a ne suka yi wa gwamnan tarba ta musamman.

Ya ce: “A ranar 18 ga watan Agustan 2023 ne Gwamnatin Dauda Lawal ta fara aikin bunƙasa birni, wanda zuwa yanzu ya yi nisa.

“Wannan aiki na bunƙasa birni yana daga cikin ƙudurin gwamnan na ganin ya yi abin da zai amfani al’umma, shi ne ma dalilin da ya sa ya ajiye komi, ya tafi domin duba yadda aikin ke tafiya.

“Har wayau, a wurin duba aikin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da an yi komi bisa ƙa’ida, domin gwamnati ce da ta zo yin aikin ceton al’umma.

“A cikin kwanaki 20 kacal, har an kammala sharar hanyoyin, an yi kwalbatoci, an kuma zuba duwatsu. Yanzu abin da ya rage kawai a shimfiɗa kwalta.

“Wannan aikin bunƙasa birni shi ne irinsa na farko a tarihin jihar Zamfara.

“Sai dai a wurin duba aikin, Gwamnan Zamfarawa, Dauda Lawal ya roƙi jama’a da su ƙara haƙuri, domin aiki ne da ke buƙatar haƙuri da sadaukarwa.”