Za mu ba da tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka wajen kama wasu masu laifi a Kano – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce tana neman wasu masu lafi biyu ruwa a jallo tare da cewa za ta bada tukwicin N500,000 kan kowannensu ga duk wanda ya taimaka da bayanai aka kama su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammed Sani Gumel ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wani babban mai laifi, Sadiq Ahmad wanda aka fi sani da Big Star, ɗaya daga cikin ɓatagarin da suka addabi al’ummar birnin Kano.

CP Gumel ya ce da daɗewa sunan Sadiq Anmad na cikin jerin sunayen waɗanda rundunar ke nema ta kama, kuma ya shiga hannu ne sakamakon harin da ya kai wa wani Abdulrahman Isah ta hanyar amfani da almakashi inda ya yi masa mummunan rauni.

Kwamishinan ya bada tabbacin ana kan gudanar da bincike wanda bayan kammalawa za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu.

Kazalika, Kwamishinan ya yi amfani da wannan dama wajen gode wa jama’ar Kano bisa haɗin kan da suke bai wa ‘yan sanda wajen gudanar da harkokinsu a jihar.

Daga nan, ya jaddada cewar akwai tukwicin N500,000 a kowanne ga duk wanda ya bada bayanan da za su taimaka wa rundunar wajen damƙe manyan masu laifin da take nema, musamman Abba Burakita daga Ɗorayi Karama Quarters da Hantar Daba daga Kwanar Disu Quarters, dukkansu mazauna Kamo Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *