03
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai kamfanin sada zumunta na X da a baya aka fi sani da Twitter Elon Musk ya ce nan ba da jimawa ba shafin zai bai wa ma'abotansa damar fara kiran waya da na bidiyo. Cikin wani saƙon X da ya wallafa Mista Musk ya ce hakan na daga cikin matakan mayar da shafin na komai-da-ruwanka. “Kiran waya da na bidiyo na nan tafe a shafin X'', kamar yadda ya rubuta ba tare da cikakkken bayani kan lokacin da za a fara amfani da su a shafin ba. Mista Musk ya ce za a…
