Za a fara kiran waya da na bidiyo a Tuwita ba tare da lamba ba – Musk

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai kamfanin sada zumunta na X da a baya aka fi sani da Twitter Elon Musk ya ce nan ba da jimawa ba shafin zai bai wa ma’abotansa damar fara kiran waya da na bidiyo.

Cikin wani saƙon X da ya wallafa Mista Musk ya ce hakan na daga cikin matakan mayar da shafin na komai-da-ruwanka.

“Kiran waya da na bidiyo na nan tafe a shafin X”, kamar yadda ya rubuta ba tare da cikakkken bayani kan lokacin da za a fara amfani da su a shafin ba.

Mista Musk ya ce za a iya samun duka kiraye-kirayen biyu a wayoyin IPhone da na Android da kamfutoci.

Ya ci gaba da cewa ba a buqatar lambar waya domin morar waɗannan sabbin tsare-tsaren da ya ɓullo da su.