EFCC ta mayar wa wata ‘yar Birtaniya Naira miliyan 25 da aka damfare ta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tatalin Arzikin Nijeriya Ta’annati EFCC ta mayar wa Christine Brown wata ‘yar Birtaniya da aka yi zambata ta intanet, kudinta dala 26,000 kimanin Naira miliyan 25.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, yana mai cewa ofishin hukumar reshen jihar Benin ya mayar da kuɗaɗen ranar Litinin.

Ya ce Misis Brown ta bayyana jin daɗinta tare da godiya ga hukumar bisa namijin ƙoƙarin da ta yi wajen mayar mata da kuɗaɗenta bayan ta fitar da rai da su a baya.

Mista Uwujaren ya ce matar mai shekara 70 ce ta miqa kokenta ga hukumar bayan an damfare ta.

Matar da shaida wa hukumar cewa ta haɗu da mutumin da ya damfare tan wanda ya ce sunansa John Barrowman a shafin intanet.

Da fari ya buƙaci yin ƙawance da ita, inda daga baya ya riƙa aike mata da buƙatar kuɗi, inda kuma ta riƙa tura masa maƙudan kuɗaɗen.

Daga ƙarshe Mista Uwajeren ya yi kira ga mutane su riƙa lura da mutanen da suke mu’amala da su a intanet, domin kauce wa faɗa wa hannun mazambata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *