Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Sarkin noman mata ta Jihar Kano Hajiya Saude Balarabe Kura, ta ce su a matsayin su na manoma mata wanda aka naɗa ta a Sarkin noman matan jihar Kano sun fara ƙirga riba a zuwan sabuwar gwamnati ta Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin a cewarta yadda wannan gwamnatin ta fara tunkarar matsalolin manoma da warware su musamman ta fuskar taki, iri, da samar da tsaro a borane da karkara wannan babbar nasara ce ga manoman Kano maza da mata da ma Nijeriya baki ɗaya.
Hajiya Saude Kura ta bayyana haka ne a tsakiyar makon da ya gabata.
Har ila yau ta ce wata babbar nasara da al’ummar Kano suka fara gani kafin kwana 100 da cikar hawa gwamnatin Kano shi ne samar da tsaro a kwaryar Kano da wajenta domin da hawan gwamna Abba Kabir ka daina jin labarin kwatar waya da hallaka mutum akan waya ga kuma samar da hasken wutar lantarki da ruwan sha da kuma kwato filaye wanda aka yi a wurare da basu dace ba kamar makarantu asibitoci, da maqabartu da aka yi gini ba bisa ƙa’ida ba duk an fara ƙwato su wannan nasara ce ga gwamnatin Abba Kabir da sauran ɗaukacin al’ummar Kano masu kishin Kano.
A ƙarshe ta yi addu’ar samun kyakkyawan nasara ga wannan gwamnatin wajen ciyar da Kano gaba da kuma addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya wanda ta ce zaman lafiya da cigaban al’umma shi ne babban arziki a ko’ina.