REB za ta fara samar da wutar lantarki ta zamani a yankunan karkara a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara ta REB Kano, Injiniya Sani Bala Ilyasu Ɗanbatta MD ya ce yanzu haka wannan hukuma ta yi nisa wajen tsare-tsare da shiri na samar wutar lantarki ta zamani mai aiki da hasken rana domin samar da wadatarciyya wutar lantarki ga al’ummar yankunan karkara da ke jihar Kano.

MD Sani Bala ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a birnin Kano a ranar Alhamis da ta gabata.

Haka kuma ya qara da cewa haɗin kan da kula da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa wannan hukuma ta hanyar sahalewa da amincewa cikin kwana ɗaya ko biyu a duk lokacin da wannan hukuma ta REB ta miƙa bunƙatun ta da gwamna Kano ke yi yasa ba da daɗewa ba za a ga canji a yankunan karkarar Kano kuma ya yabawa Kano kan ba shi wannan damar a naɗa shi shugaban wannan hukuma ta samar da wutar lantarki a yankunan karkara kuma dama manufar gwamnatin kwankwasiyya na ciyar da alumma gaba ta kowanne fani na rayuwar alummar Kano.

A qarshe ya bayyana takaicinsa akan yadda ya samu wannan hukuma na rashin kayan aiki a maaikatar kamar tsanin hawa sama don yi aiki da belt belt na ɗaurawa ga maaikatan ga kuma rashin ruwa da sauran matsaloli a wannan hukuma ta REB da ya samu, ya ce wani abun takaici yadda aka bar taransufomomi a maaikatar masu yawa baa rabawa alumma ba har sun fara lalacewa, amma abin farin ciki da ƙarfafa gwiwa shi ne ina sanar da gwamna Kano waɗannan matsaloli da neman gyaran su gwamna ya amince yanzu duk an shawo kan wasu matsalolin na wannan ma’aikata mai kwararrun maaikata da kishi domin ciyar da yankunan karkara dama kano baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *