Kishi da sanin makama ne tushen nasarar Hukumar Alhazan Kano – Kabir Panda

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban kula da ayyuka na hukumar jin daɗin alhazan Jihar Kano, Alhaji Kabiru Muhammad Panda ya bayyana cewa kyakkyawan shugabanci mai cike da kishin al’umma da sanin makama da tsoron Allah na Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya naɗa Alhaji Laminu Rabiu Ɗan Baffa a matsayin shugaban hukumar alhazai da ake cewa goga kasan hanya, shi ne tushen samun kyakkyawan nasara a aikin Hajji da ya gabata a wannan shekara ya sa hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta samu gagarumar nasara na kai alhazai ƙasa mai tsarki su 6567 cikin nasara da kuma dawo da su cikin nasara.

Har ila yau ya ce sanin makama na Darkta Janar Alhaji Laminu Rabiu Ɗan Baffa na kafa kwamitoci masu yawa da suka haɗa da na lafiya, zirga-zirga, abinci, tsaro, yaɗa labarai, tattara bayanai da sauransu da sauran kwamitoci da suka yi aiki ba dare ba rana a Kano gida Nijeriya da kuma can ƙasa mai tsarki wannan ya haifar da gaggarumar nasara a wannan shekara musamman ganin yadda shi DG Alhaji Laminu ana naɗa shi ya tafi sansanin na Kano wajen warware duk wata matsala ta masaukin alhazai musamman abin da ya shafi samar da injinan wutar lantarki da gyaran ɗakuna da banɗakuna da dai sauran gyara ɗaukanci matsalolin da ya samu a ciki ƙanƙanin lokaci ya kawar da su domin samun nasarar wannan aiki.

A ƙarshe Alhaji Kabiru Muhammad Panda ya ce wannan hukuma ƙarƙashin shugabanci shugabanta Alhaji Yusuf Lawan da DG Alhaji Laminu Baba Ɗanbaffa da sauran masu ruwa da tsaki tsayuwar su da aikin su ya samo asali ne daga haɗin kai da goyan baya da kishi na Gwamnan Kano ga alhazan Kano da ma sauran al’ummar Kano wanda da a ce ba wannan Gwamnatin ta Injinya Abba ba ce da Kanawa suka zaɓa da ba wannan zancen ake ba kuma raba wa alhazan Kano kuɗin riyal da Gwamnan Kano ya yi shi ma abin godiya ne ga Allah da kuma gwamnatin jihar Kano.