Shettima na da halayyen jagoranci, inji Sheriff

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon gwamnan Borno, Ali Sheriff, ya bayyana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima a matsayin jagora wanda ke misalta muhimman manufofin jagoranci nagari.

Sheriff ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Shettima a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya godewa shugaban qasa Bola Tinubu bisa samun Shettima wanda ya cancanci zama mataimakinsa.

Sheriff ya ce, “Na zo nan ne domin ganin Mataimakin Shugaban Nijeriya, wanda ƙanena ne, wanda na yi aiki tare da shi sosai lokacin da nake Gwamnan Jihar Borno.

“Don haka na zo ne don in sa masa albarka a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya da kuma yi masa fatan alheri.

“Ka sani Allah mai iko ne. A yau, wani da ya yi aiki tare da ni sama da shekaru 10, a yau shi ne na biyu a Nijeriya.”

Jigon na APC ya tuna da alfahari cewa ya miƙa wa Shettima kujerar gwamnan Borno a shekarar 2011, inda ya ƙara da cewa mataimakin shugaban asar yayi aiki tare da shi a matakai daban-daban.

Sheriff ya ƙara da cewa, “Na mika masa muƙamin gwamnan jihar Borno, ya yi aiki tare da ni a matakai daban-daban kuma ya baje kolin shugabanci a tarihi.

“Kuma ta hanyar duba, shugaba Bola Tinubu ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *