Labarai

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a iftila’in masallaci a Zariya

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a iftila’in masallaci a Zariya

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 10 ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya sannan da dama sun jikkata sakamakon rikitowar wani ɓangare na ginin Babban Masallacin Zariya da ke Kaduna. Da yake tabbaar da aukuwar iftila'in da ya auku a ranar Juma'a, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce lamarin ya faru ne da la'assariyar wannan rana. Ya ce, “Tun farko, jiya mun lura cewa bangon ginin ya tsage inda aka fara shirin ɗaukar injiniyoyin da za su yi aikin gyara kafin daga bisani wannan iftila'in ya auku." Bayan miƙa ta'aziyya ga 'yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin,…
Read More
Gwamnan Zamafara ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na ZAYOSAP

Gwamnan Zamafara ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na ZAYOSAP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ƙaddamar da shirin tsaftace muhalli na Zamfara Youth Sanitation Programme’ (ZAYOSAP) domin tsaftace babban birnin Jihar Zamfara da kewaye. Bikin ƙaddamar da shirin ya gudana ne ranar Juma'a a tsohon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan ya jaddada cewa shirin yana daga cikin shirye-shiryen da gwamnatinsa ta ke da su domin tabbatar da tsaftar muhalli da kiyaye yaɗuwar cututtuka a jihar. Wata sanarwar manema labarai da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce an ƙirƙire shirin ne…
Read More
Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar NAYES da sauran hukumomin tsaro a Nasarawa – G.M Labaran Maina

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar NAYES da sauran hukumomin tsaro a Nasarawa – G.M Labaran Maina

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Janaral Manaja na hukumar tsaro na gwamnatin jihar Nasarawa wato Nasarawa Egency For Youth Empowerment Scheme (NAYES) a turance, Abdullahi Labaran Maina ya yi kira na musamman ga jami’an hukumar ta NAYES a jihar baki ɗaya su tabbatar suna cigaba da kasancewa jami’an hukumar nagari a duk inda suke gudanar ayyukansu a faɗin jihar. Janaral Manajan, Abdullahi Labaran Maina ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishinsa dake hedikwatar hukumar ta NAYES a garin Lafiya babban birnin jihar ranar Talata na makon nan da ake ciki. Ya…
Read More
Rufe kan iyakokin Nijeriya ya jawo durƙushewar kasuwanci da masana’antu a Arewa – Ɗanpass

Rufe kan iyakokin Nijeriya ya jawo durƙushewar kasuwanci da masana’antu a Arewa – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Rufe kan iyakokin ƙasar nan ya taimaka wajen kassara harkokin kasuwancin al'ummar Arewacin ƙasar nan musamman ma jihar Kano da take cibiyar kasuwanci. Fitaccen ɗan kasuwa ɗaya daga cikin dattawan Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce sai da suka ja hankalin tsohon shugaban qasa Muhammad Buhari akan kar a rufe kan iyakokin nan na Arewa, suka kuma yi kira akan a buɗe bayan an rufe amma ba a ji ba sai ga shi kasuwanci ya shiga halin ha'ula'i a Kano da Arewa bakiɗaya. Ya yi nuni da…
Read More
‘Yan bindiga sun sace Sarkin Gurku a Jihar Nassarawa

‘Yan bindiga sun sace Sarkin Gurku a Jihar Nassarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Nassarawa ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun ɗauke Sarkin Gurku da iyalinsa. Rundunar ta ce da misalin ƙarfe goma na dare, maharan, waɗanda ake zargin masu satar mutane ne ɗauke da bindigogi suka kutsa fadar mai martaba Sarkin Gurku, mai daraja ta ɗaya, Alhaji Jibrin Mohammed, bayan sun kaikaici lokacin da aka watse daga fada, wadda ke da tazarar kilomita goma da marabar Gurku da ke jikin babbar hanyar da ta tashi daga Abuja ta dangana da Keffi, inda suka tafi da shi da mai ɗakinsa. Kakakin rundunar…
Read More
Likitoci sun janye aniyarsu ta gudanar da zanga-zanga

Likitoci sun janye aniyarsu ta gudanar da zanga-zanga

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta dakatar da shirinta na gudanar da zanga-zangar gama-gari don nuna wa gwamnati rashin jin daɗinta na rashin cim ma buƙatunta. NARD ta janye aniyar tata ne bayan tattaunawar sirrin da suka yi da wasu jigajigan Majalisar Dattawa a ranar Talata. Shugaban NARD na Ƙasa, Emeka Orji, shi ne ya bayyana haka a zantawar da aka yi da shi ta tarho da safiyar wannan Larabar. Sai dai, Orji ya ce za a yi zaman waiwaiye nan da sa'o'i 72 masu zuwa. "Mun gana da Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Masu Rinjaye da…
Read More
Ƙaƙaba wa Nijar takunkumai ra’ayin ECOWAS ne ba nawa ba – Tinubu

Ƙaƙaba wa Nijar takunkumai ra’ayin ECOWAS ne ba nawa ba – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa wa'adi da kuma takunkuman da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da ya auku a ƙasar, matakai ne da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta cim ma amma ba ra'ayin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ko Nijeriya ba. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Mr Ajuri Ngelale shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Talata. Ngelale ya ce kuskure ne danganta matakan na ECOWAS da Shugaba Tinubu a matsayin shi kaɗai…
Read More
Yajin Aiki: Gwamnati ta roƙi likitoci da su koma bakin aiki don ceton rayuka

Yajin Aiki: Gwamnati ta roƙi likitoci da su koma bakin aiki don ceton rayuka

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta roƙi Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD) a kan ta dakatar da yajin aikin da mambobinta ke yi don ceto rayukan marasa lafiya da ke kwance a asibitocin faɗin ƙasar. Babbar Sakatatiyar Ma'aikatar Ƙwadago da Bada Aiki, Mrs Daju Kachallom ce ta yi wannan roƙo sa'ilin da take zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja. Ta ce likitocin su dubi Allah su dubi Annabi, ka da su bari a ci gaba da samun asarar rayukan 'yan Nijeriya a asibitoci saboda rashin samun kulawa. Kachallom ta bai wa likitocin tabbatacin Gwamnatin Tarayya na yin dukkan…
Read More
Mutum 45 da Majalisar Dattawa ta tabbatar da su ministoci

Mutum 45 da Majalisar Dattawa ta tabbatar da su ministoci

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan tantance su da ta yi, a ƙarshe Majalisar dattawa ta tabbatar da mutum 44 a matsayin ministoci. Waɗanda lamarin ya shafa su ne: -Mohammed Idris Malagi, Neja-Sanata Aliyu Sabi Abdullah, Neja-Nyesom Wike, Ribas-Ekperikpe Ekpo, Akwa Ibom-Sanata Heineken Lolokpobri, Bayelsa-Betta Edu, Cross River-John Enoh, Cross River-Abubakar Momoh, Edo.-Tahir Mamman, Adamawa-Yusuf M Tuggar, Bauchi-Mohammed Ali-Pate, Bauchi-Abubakar Kyari, Borno-Alkali Ahmed Saidu, Gombe-Uba Maigari Ahmadu, Taraba-Sanata Ibrahim Geidam, Yobe-Mohamed Badaru, Jigawa-Mariya Bunkur, Kano-Abdullahi T Gwarzo, Kano-Ahmad Dangiwa, Katsina-Hanatu Musawa, Katsina-Yusuf Tanko Sununu, Kebbi-Atiku Bagudu, Kebbi-Bello M. Goronyo, Sokoto-Mohammed Bello Matawwalle, Zamfara-Hon Nkiru Onyejiocha, Abia-Uju Ohaneye, Anambra-Sanata David Umahi, Ebonyi-Uche…
Read More