Likitoci sun janye aniyarsu ta gudanar da zanga-zanga

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta dakatar da shirinta na gudanar da zanga-zangar gama-gari don nuna wa gwamnati rashin jin daɗinta na rashin cim ma buƙatunta.

NARD ta janye aniyar tata ne bayan tattaunawar sirrin da suka yi da wasu jigajigan Majalisar Dattawa a ranar Talata.

Shugaban NARD na Ƙasa, Emeka Orji, shi ne ya bayyana haka a zantawar da aka yi da shi ta tarho da safiyar wannan Larabar.

Sai dai, Orji ya ce za a yi zaman waiwaiye nan da sa’o’i 72 masu zuwa.

“Mun gana da Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Masu Rinjaye da Mai Tsawatarwa da kuma Shugaban Marasa Rinjaye,” in ji Orji.

Tun farko, a wannan Larabar likitocin suka shirya fara gudanar da zanga-zangar lumana muddin gwamnati ta gaza cim ma buƙatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *