Labarai

Harin Yauri: An kuɓutar da malamai 2, ɗalibai 6

Harin Yauri: An kuɓutar da malamai 2, ɗalibai 6

Daga AMINA YUSUF ALI Alamu sun nuna malamai biyu da kuma ɗalibai shida na Federal Government College (FGC) Yauri da aka yi garkuwa da su, sun kuɓuta. Bayanai sun tabbatar da cewa an samu nasarar kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa ne sakamakon kwanton ɓaunan da da jami'an tsaro suka yi wa 'yan bindigar da suka kai wa makarantar hari. Tun bayan aukuwar harin da aka kai FGC Yauri sama da sa'o'i 24 da suka gabata, har yanzu babu wani bayani da aka fitar a hukumance kan batun, walau daga gwamnatin jihar Kebbi ko 'yan sanda. Ɗalibai kimanin su talatin…
Read More
Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da shirin bada ilimi kyauta ga marayu

Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da shirin bada ilimi kyauta ga marayu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙarshen makon jiya ne kansilan Kano, Honorabul Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da raba tallafi ga marayu 10 da aka samar wa gurbin karatu da ɗaukar nauyin su a 'Ihya'us Sunna Science and Commercial College' tare da bada tallafin N20,000 don ɗinka masu kayan makaranta. Shirin wanda ke ƙarkashin kwamitin Hajiya Bilkisu Yusuf Ali da ake wa laƙabi da 'Guringawa Education Promotion Committee' a turance zai duba makarantun kuɗi da ke cikin mazaɓar don samun gurbi na malamai da ɗalibai, sai kuma gidauniyar kansila ta bayar da tallafi. Haka kuma Muslihu Yusuf Ali,…
Read More
Za a rataye ɗan shekara 22 saboda fashi da makami a Ekiti

Za a rataye ɗan shekara 22 saboda fashi da makami a Ekiti

Daga WAKILINMU Babbar Kotun jihar Ekiti mai zamanta a Ado-Ekiti, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Kehinde Olajide hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda aikata laifin fashi da makami. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta saki wasu 'yan gida ɗaya da aka alaƙanta su da fashin, wato Kareem Azeez mai shekara 24 da Bamisile Lateef ɗan shekara 28 da kuma Adebayo Basiru ɗan shekara 25. Yayin da yake yanke hukuncin ran Alhamis da ta gabata, Mai Shari'a Lekan Ogunmoye, ya ce masu gabatar fa ƙara sun gabatar da gamsassun hujjojin aikata fashi da makami…
Read More
Bai kamata mu yi saurin mantawa da gudunmawar Kaunda ba – Buhari

Bai kamata mu yi saurin mantawa da gudunmawar Kaunda ba – Buhari

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasar Zambiya, Kenneth Kaunda, a matsayin "Ɗaya daga cikin manyan shugabannin Afirka da na duniya baki ɗaya da ke ƙaunar ƙasarsa da mutanensa sosai. Buhari ya ce labarin rasuwar Kaunda ya kaɗa shi matuƙa saboda sanin irin gudunmawar da ya bai wa ƙasarsa Zambiya da ma Afirka baki ɗaya a halin rayuwarsa. A sanarwar da ta tafito ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, "Ba za mu yi saurin manta gwagwarmayar Kaunda ba wajen ƙwato wa Zambjya 'yanci daga Afirka ta Kudu da kuma tsohuwar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ba Kanawa 320 aikin duba shiri tare da na’urori

Gwamnatin Tarayya ta ba Kanawa 320 aikin duba shiri tare da na’urori

Daga AISHA ASAS Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da shirin raba takardun kama aiki tare da na'urorin duba aiki ga waɗanda aka horas domin sanya ido kan ayyukan ma'aikatar a jihar. An gabatar da taron a ɗakin taro na 'Coronation' da ke cikin gidan gwamnati Hall a Kano a ranar 15 ga Yuni, 2021. Ministar, wadda Babban Sakatare a ma'aikatar, Bashir Nura Alƙali ya wakilta a taron, ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro Shirin Inganta Rayuwar Jama'a, wato 'National Social Investment Programme' (NSIP) ne a cikin 2016 domin a fidda…
Read More
Gobe Barno za ta karɓi baƙuncin Buhari

Gobe Barno za ta karɓi baƙuncin Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI Ana sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar Barno ran Alhamis idan Allah ya kai mu. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, shi ne ya bayyana haka yayin jawabin da ya yi wa 'yan jihar kai tsaye a kafar yaɗa labarai a Maiduguri. Tare da kira ga talakawansa da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata domin tarbar babban baƙon nasu. A cewar Zulum Buhari da tawagarsa za su ziryaci Barno ne domin la'akari da sha'anin tsaro na yankin Arewa-maso-gabas, kana ya ƙaddamar da tarin ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar a tsakanin shekaru…
Read More
Almundahana: Yadda muka cafke ministar da ta sayi gida na Dala milyan 37.5 ta bayan fage – EFCC

Almundahana: Yadda muka cafke ministar da ta sayi gida na Dala milyan 37.5 ta bayan fage – EFCC

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya labarta yadda wata minista ta sayi gida na maƙudan kudi Dala milyan $37.5 daga hannun wani banki sannan ta biya rabin kuɗi Dala milyan $20 kuɗi hannu. Bawa ya ba da wannan labari ne ba tare da ya bayyana sunan ministar da lamarin ya shafa ba, haka ma bai bayyana ko har yanzu ministar na kan kujera ko kuwa a'a ba. Shugaban EFCC ya yi wannan bayanin ne yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar talabijin…
Read More
Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona milyan 3.92 a Agusta – Gwamnati

Nijeriya za ta karɓi rigakafin korona milyan 3.92 a Agusta – Gwamnati

Daga AISHA ASAS Ana sa ran Nijeriya ta karɓi ƙarin aullurar rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca guda milyan 3.92 ya zuwa farkon Agusta. Shugaban Hukumar Bunƙasa Lafiya a Matakin Farko, Dr Faisal Shuaib ne ya bayyana haka a Talatar da ta gabata a Abuja. Sai dai bai bayyana takamammiyar ranar da maganin zai shiga hannun Nijeriya ba. Ya ce, “Mun samu labarin Nijeriya za ta samu rigakafin korona na Oxford/AstraZeneca guda milyan 3.92 ya zuwa ƙarshen Yuli ko farkon Agusta." Ya ƙara da cewa, "Idan muka samu ƙarin bayanai game da takamammiyar ranar da za a karɓi maganin, za mu bayyana…
Read More
Bello ya koka kan yadda ‘yan siyasa da jami’an gwamnati ke saida wa ‘yan fashi bayanan sirri

Bello ya koka kan yadda ‘yan siyasa da jami’an gwamnati ke saida wa ‘yan fashi bayanan sirri

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce wasu 'yan siyasa da na kusa da gwamnati sun zaɓi zama 'yan leƙen-asiri ga 'yan bin bindigar da suka addabi jihar saboda kuɗi inda sukan saci bayanan sirri na gwamnati suna kai wa ɓarayin. Gwamna Bello ya bayyana haka ne a Talatar da ta gabata a lokacin da yake ƙaddamar da rundunar tsaro ta musmman mai jami'ai 161 domin yaƙi da rashin ɗa'ar matasa a Minna babban birnin jihar. A cewarsa, "Akwai 'yan siyasa da wasu na kusa da gwamnati da ke satar bayanai suna kai wa ɓarayin. Ko da taro…
Read More
NUJ ta samu tabarrukin Janar Babangida a Minna

NUJ ta samu tabarrukin Janar Babangida a Minna

Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida, ya bai wa Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) Reshen Jihar Neja, tabbacin mara mata baya don taimaka mata wajen cim ma manufofinta. Babangida ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin da tawagar sabbin shugabannin NUJ na jihar Neja ta ziyarce shi a gidansa da ke Minna, a Lahadin da ta gabata. Tsohon shugaban ya ce ya yaba da ziyarar 'yan jaridar ƙarƙarshin jagorancin shugabansu na jiha, Comrade Abu Nmodu. Tare da kira a gare su da su kasance masu aiki da gaskiya a kowane lokaci. Haka nan, ya shawarce…
Read More