Labarai

Yadda maganin gargajiya ya yi sanadin mutuwar mutum 10 ‘yan gida ɗaya a Kwara

Yadda maganin gargajiya ya yi sanadin mutuwar mutum 10 ‘yan gida ɗaya a Kwara

Daga WAKILINMU Al'ummar ƙauyen Biogberu da ke yankin ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara, sun faɗa wani hali na tashin hankali biyo bayan wasu 'yan gida ɗaya su goma da suka kwanta dama ɗaya bayan ɗaya a ƙauyen sakamakon wani maganin gargajiya da suka kwankwaɗa. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna wannan al'amari mai gigitarwa ya faru ne ran Juma'a ta makon jiya. Wata majiya mai tushe ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta ce wasu 'yan ƙauyen su biyu, Okosi Musa da Worugura Julin, su ne suka bai wa wata mata mai suna Pennia Bonnie maganin gargajiya…
Read More
Babu mai raba mana Nijeriya, cewar Ganduje

Babu mai raba mana Nijeriya, cewar Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce duk da irin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta, za ta ci gaba da kasancewa ƙasa dunƙulalliya. Ganduje ya bayyana haka ne a Kano a matsayin martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi a ƙasa inda wasu 'yan ƙasa ke rajin ɓallewa daga Nijeriya don kafa tasu ƙasar. Gwamnan ya ce yana da yaƙinin Nijeriya ba za ta rabe ba komai ƙalubalen da take fuskanta. Ya ci gaba da cewa ba ya son yin magana game da masu neman a raba ƙasa, saboda a cewarsa masu wannan buƙata…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da kwamitin shirin raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara

Buhari ya ƙaddamar da kwamitin shirin raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara

Daga UMAR M. GOMBE A Talatar da ta gabata ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kwamitin da aka ɗora wa alhakin sanya ido kan shirin rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ana sa ran ya raba 'yan Nijeriya miliyan 100 da fatara. Buhari ya sha alwashin gwamnatinsa za ta fito da dabarun da za su taimaka mata wajen kuɓutar da 'yan Nijeriya milyan 100 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru goma masu zuwa. A jawabinsa yayin ƙaddamar da kwamitin, Buhari ya bayyana dabarar da kwamitin NPRGS za ta…
Read More
Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya kan ƙarin kasafin biliyan N895

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya kan ƙarin kasafin biliyan N895

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Ahmad Lawan, ya karanta wa majalisa wasiƙar da Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar yana neman amincewarta kan ƙarin kasafin kuɗi na biliyan N895. Lawan ya karanta wasiƙar Shugaban Ƙasar ne yayin zaman da majalisar ta yi a Talatar da ta gabata. Da ma dai kafin wannan lokaci, Majalisar Zartarwa ta yi na'am da ƙarin kasafin da Buhari ya nema. Bayanai sun nuna za a yi amfani da wani kaso mai tsoka daga kasafin wajen sayo wa sojoji ƙarin kayan aiki domin ƙara musu ƙarfi wajen yaƙi da ta'addanci da 'yan…
Read More
Buhari ya amince da kashe bilyan N18 don gina sabbin jami’o’i huɗu a sassan ƙasa

Buhari ya amince da kashe bilyan N18 don gina sabbin jami’o’i huɗu a sassan ƙasa

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe kuɗi Naira biliyan 18 domin gina jami'o'in ƙwararru guda huɗu a faɗin ƙasa. Gwamnati ta bayyana haka ne a Litinin da ta gabata, inda ta ce jami'o'in da za a gida sun haɗa da ta fasaha da za a gina Jigawa da Akwa Ibom, sai kuma ta kiwon lafiya da nazarin ingancin abinci da magunguna da za a gina a Azare, jihar Bauchi da Ila Orangun, jihar Osun. Da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce…
Read More
El-Rufai ya rantsar da wasu manyan jami’an gwamnati

El-Rufai ya rantsar da wasu manyan jami’an gwamnati

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna da Shugaban Hukumar Kula da Kwangiloli ta Jihar Kaduna da kuma wasu sababbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin Jihar a gidan gwamnati da ke Kaduna. Ranar Litinin Gwamnan ya rantsar da jami'an da lamarin ya shafa da suka haɗa da: Dakta Saratu Binta Dikko Audu - Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna.Injiniya Sanusi Aminu Yero - Shugaban Hukumar Kula Kwangiloli ta Jihar Kaduna.Adamu Atama - Babban Sakatare.Abubakar Abba Umar - Babban Sakatare.Balarabe Wakili -…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 40 masu ciwon sikila sun nemi taimakon Buhari – Ƙungiya

‘Yan Nijeriya miliyan 40 masu ciwon sikila sun nemi taimakon Buhari – Ƙungiya

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Wata cibiya ta neman taimako ga masu ciwon sikila daga gwamnati da daukacin al’umma ta gabatar da kokenta ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na kawo ɗauki ga masu fama da wannan ciwo kimanin su miliyan 40 da ke sassa daban-daban na ƙasar. Kamar yadda cibiyar ta ce, masu wannan ciwo su na ta mutuwa, saboda rashin samun ingantaccen abinci, haɗi da rashin samun magunguna da ke rage raɗaɗin ciwon na sikila. Da suke gabatar da koken nasu a daidai lokacin bikin shekara-shekara na tunawa da ciwon na sikila a Bauchi, majinyatan sun bayyana hali…
Read More
Harin Yauri: An ceto ƙarin malami ɗaya, ɗalibai uku

Harin Yauri: An ceto ƙarin malami ɗaya, ɗalibai uku

Daga AISHA ASAS Sojojin Nijeriya ƙarƙashin shirin Operation HADARIN DAJI tare da taimakon sojojin sama, sun yi nasarar ceto ƙarin waɗanda aka yi garkuwa da da su a FGC Birnin Yawuri. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna waɗanda aka kuɓutar ɗin sun haɗa da malami ɗaya da ɗalibai uku, an kuɓutar da su ne a Makuku. Sanarwar da ta fito daga Daraktan Sashen Hulɗa da Jama'a na Sojojin Nijeriya, Brigadier General Onyema Nwachukwu, ta nuna baya ga kuɓutar da waɗanda lamarin ya shafa, haka nan jami'an sun kashe ɗaya daga cikin ɓarayin sannan sun ƙwato babura guda tara daga…
Read More
Zulum ya amshi umarnin Buhari na dawo da aikin gona  a yankin Mulai-Dalwa

Zulum ya amshi umarnin Buhari na dawo da aikin gona a yankin Mulai-Dalwa

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara a ƙauyukan Mulai da Dalwa tare da ganawa da jami'an tsaro don samar da matakan da suka dace wajen farfaɗo da harkar noma a ƙauyukan. A Lahadin da ta gabata Zulum ya yi wannan ziyarar a matsayin wani mataki na cika umarnin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya bayar sa'ilin da ya ziyarci jihar Alhamis da ta gabata, inda ya buƙaci jami'an tsaro su yi aiki tare da gwamnatin jihar wajen samar da tsare-tsaren da za su bai wa jama'ar ƙauyukan damar komawa gona ba tare da wata fargaba…
Read More