Babban Labari

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda

Daga Umar Mohammed Gombe Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi. A wani zama da kotun ta yi na mutum uku karkashin jagorancin Jastis Stephen Adah, a yau Juma'a da yamma, akan hukuncin da ta yanke, ya yi watsi da daukaka karar da Maryam Sanda ta shigar gaban kotun bisa rashin cancanta. A farkon wannan shekarar idan za a tuna, Mai Shari'a Yusuf Halliru na Babbar Kotu a Abuja da ke Maitama, ya yanke mata hukuncin kisa ta…
Read More