CBN ya haramta wa masu POS canjin sabbin kuɗi a Abuja da Legas

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya haramta wa masu POS a Abuja da Legas harkar musayar sabbin takardun Naira da tsoffi.

Cikin sanarwar da ya fitar, CBN ya zayyana wasu ƙa’idoji game da shirin musayar sabbin kuɗin don waɗanda aka sahale wa su kiyaye.

Sanarwar ta nuna wasu bankuna biyar kaɗai aka amince wa gudanar da wannan shiri, wato Access Bank Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa Plc, First Bank sai kuma First City Monument Bank.

“Ba duka ejent za su shiga shirin ba, sai wasu zaɓaɓɓu waɗanda aka miƙa bayanansu ga CBN da kuma bankunan da aka zaɓa don shirin,” in ji sanarwar.

Game da jihohin da aka yarje wa shiga shirin kuwa, sanarwar ta ce “Zaɓaɓɓun ejent na jihohi 36 na iya shiga shirin amma ban da Legas da Abuja.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙananan ejent za su miƙa bayanan nasu ne ta hannun manyan ejent na gaba da su ko kuma banukunan da suke mu’amala da su don tantancewa duk lokacin da suka je karbar sabbin kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *