CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin ɗari.

Gwamnan CBN, Dr. Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa shawarar rage kuɗaɗen ruwa ta biyo bayan ci gaba da saukar hauhawar farashin kayayyaki da aka samu cikin watanni biyar da suka gabata.

Haka kuma, bankin ya ce ya rage ƙa’idar kuɗaɗen ajiya ga manyan bankuna zuwa kashi 45, yayin da aka bar na bankunan kasuwanci a kashi 16.

Kwamitin manufofin kuɗi na Babban Bankin ya sanar da wata sabuwar ƙa’idar ajiyar kuɗi a ɓangaren gwamnati.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS ta sanar da ƙaruwar arzikin cikin gida na ƙasar a rubu’in na biyu na shekarar 2025.

By ukarofi