CBN ya wayar da kan masu ta’ammali da POS a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Babban Bankin Najeriya CBN ya gudanar da taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya ga ƙungiyoyin dake harkokin kasuwancin POS reshen jihar Zamfara kan mahimmancin shirin eNaira da canjin kuɗaɗen da ake ciki.

Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na Maryam da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Alhamis wanda ƙungiyar masu gudanar da POS reshen jihar Zamfara suka shirya a hukumance.

A nasa jawabin, Shugaban Babban Bankin na CBN reshen Gusau, Malam Buhari Abbas, ya ce ɗaya daga cikin dalilan bullo da tsarin eNaira da kuma sauya fasalin wasu kudaden Najeriya da babban bankin Najeriya ya yi shi ne don rage yawan yawo da kuɗaɗen da ke hannun ‘yan Najeriya.

Wani dalili kuma a cewarsa shi ne, tsarin eNaira, da sake fasalin takardun kuɗi na N1000, N500, da N200 zai zama ma’auni wajen magance cin hanci da rashawa, rashin tsaro da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.

A cewarsa, tuni Babban Bankin Nijeriya ya umarci bankunan kasuwanci da suka haɗa da Zenith, access, UBA, FCMB da kuma First bank da su rika bayar da sabbin takardun kuɗi ga ƙungiyar masu gudanar da POS a jihar Zamfara waɗanda suka yi rajista da bankunan guda biyar domin su inganta kasuwancin su.

“Ina so in yi kira ga ɗaukacin ‘yan kungiyar POS Operators na Zamfara da suka yi rajista da bankunan kasuwanci da aka ambata da su je kai tsaye ga waɗannan bankunan su karbi sabbin takardun kuɗaɗe sannan su shigarda tsofaffin takardun dake hannunsu wanda CBN ya amince da su ga bankunan.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani banki da ya ki sauraron ‘yan POS to a kai rahoto ofishinsa da gaggawa domin ɗaukar matakin da ya dace.” Inji shi.

Abbas ya ci gaba da cewa, babban laifi ne rashin karɓar tsohon takardar Naira kafin ranar 31 ga watan Janairu kamar yadda CBN ta tsara, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana so ya ki amincewa da tsohuwar takardar Naira a matsayin takardar kudi kafin ranar 31 ga Janairu to ‘yan sanda su kama shi domin ɗaukar matakin da ya dace.

Ya umurci ma’aikatan POS na jihar da su tabbatar sun karɓi tsofaffin takardun kuɗi na Naira daga kwastomominsu kafin ranar 31 ga watan Janairu kamar yadda babban bankin ƙasar ya tanada.

Kwantirolan ya umurci mambobin ƙungiyar ma’aikatan POS na jihar Zamfara da su haɗa kai da gwamnatin tarayya, CBN da kuma bankunan kasuwanci a ƙoƙarinsu na daidaita tattalin arzikin ƙasa.