NUJ ta cire ma’aikatan NOA daga jerin ‘ya’yanta

Daga RABIU SANUSI a Kano

Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta cire ma’aikatan Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA) daga cikin jerin ‘ya’yanta tare da aiki da ita.

Batun na zuwa ne daga shugaban NUJ na Ƙasa, Mr Chris Isuzugo, a yayin taron wakilan ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a ranakun Laraba da Alhamis a Jihar Kano cikin makon nan.

Taron wakilan na musamman ya gudana ne a ɗakin taro na The Afficent Event Center da ke Nasarawa GRA a Ƙaramar Hukumar Nasarawa a cikin Birnin Kano.

Hakan ya biyo bayan amincewar wakilan ƙungiyar a taron, yayin da za a amince da aikin shugabanninsu.

Haka zalika taron ya bayyana sabuwar dokar fitar da dukkan wasu  jami’an hulɗa da jama’a na ma’aikatu da sauran hukumomin, yayin da aka bayyana cewa, su ba ’yan jarida ba ne. Don haka daga yanzu su ma ba ’yan ƙungiya ne ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *