Tsohon gwamnan Adamawa, Bindow ya fice daga APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya fice daga Jam’iyyar APC.

Bindow ya fice daga jam’iyyar ne a hukumance ta wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar APC na gundumar Kolere, ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa, mai kwanan wata 20 ga watan Janairu, 2023, wacce Manhaja ta samu kofi a ranar Talata.

Bindow, wanda bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, ya ƙara da cewa “magoya bayansa masu aminci’ a faɗin jihar za su bi shi wajen ficewa daga Jam’iyyar APC ta yadda za su jajirce wajen ganin an gina Jihar Adamawa.

A cewar tsohon gwamnan, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta ‘Sardaunan Mubi’, ya yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar APC ne sakamakon rashin samun sahihin sulhu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a Jihar Adamawa, tun bayan shan kaye da jam’iyyar ta sha a 2019 a babban zave da kuma sakamakon zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC na 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *