Mun ɗaura ɗamarar kawo sauyi ga ‘yan kasuwa a Kano – Alkamatu

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Shugaban Kamfanin Alkamatu Brain Box Solution, wato matashin nan mai rajin ganin matasa da sauran al’umma sun samu damar tsayawa da ƙafafunsu, Kwamared Alkamatu Hussain Abdulkadir ya ce shirinsu ya kankama na ganin a taimaka wajen kanikancin kasuwancisu.

Alkamatu ya ce lallai babu abinda ke gabansu yanzu haka da ya wuce ganin yankin Arewa ya ci gaba wajen harkokin kasuwanci da sauran hanyoyin dogaro da kai.

Matashin da yake taka rawar gani wajen taimakon jama’a a Jihar Kano dama makwabtan jihohin Kano ya tabbatar da cewa sanin kowa ne kamar yadda ɗan Adam da dabbobi idan sun yi rashin lafiya ake ba su kulawa ya sa shi ma kasuwanci na da buƙatar masana da za su iya kanikancin sa.

“Ya zuwa yanzu mun kusan kammala binciken yadda za mu taimaki dukkan abinda muka zo da su don ganin an ɗebi marasa lafiya irin na kasuwanci don ba su magani.”

Alkamatu ya kuma buƙaci ‘yan kasuwar da suke fuskantar matsalolin da su ƙoƙarta ganin sun samu masani da za su taimaka masu wajen samar da cigaba da warware masu ƙalubalen.

Daga ƙarshe ya yi nuni da irin yadda komai ya canza kama daga cimarmu da sitirarmu har ma da ababen hawanmu.