Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya gamu da cikas

Daga WAKILINMU

Jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari a yankin Kubwa da ke Abuja.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a a lokacin da jirgin ya kusa kaiwa tashar da zai tsaya a Abuja.

Bayanai sun nuna ƙafafun kan jirgin ne suka goce daga kan layi lamarin da ya haifar da jirkicewar kan jirgin gefe guda.

Sai dai babu wani cikakken bayani da ke nuna an jikkata a hatsarin.

Babban Daraktan Jukumar Sufurin Jirgin Ƙasa (NRC), Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Tare da cewa suna kan tattara bayanai kan abin da ya faru.

Wannan al’amari na zuwa ne mako guda bayan da wani jirgin ƙasan na Najeriya ya kauce hanya a jihar Kogi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Warri daga Itakpe.