Boko Haram ta kashe mayaƙanta sama da 300 da suka yi niyyar miƙa wuya a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu kwamandojin Boko Haram/ISWAP da ba su tuba ba sun kashe dakarunsu sama da 300 da iyalansu da ke fitowa daga dajin Sambisa da nufin miƙa wuya a Jihar Borno.

Kwamandojin dai sun katse hanzarin mayaƙan ne da nufin kawo cikas kan ƙoƙarin tattaunawar da suke yi da gwamnatin jihar.

Mai ba gwamnan Jihar Borno shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi (mai ritaya), ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Maiduguri ranar Alhamis.

A cewarsa, sama da mayaƙan Boko Haram 90,000 da iyalansu ne ya zuwa yanzu suka miƙa wuya ga gwamnatin jihar Borno a cikin watanni 17 da suka gabata tun bayan fara tattaunawar zaman lafiya da ake yi da su.

Ya yi nuni da cewa, kaso 95 cikin 100 na kwamandojin Boko Haram ne ake kashewa ko dai ta hanyar ayyukan soji ko kuma ta hanyar faɗa tsakanin vangarorin da ke gaba da juna.

Birgediya Janar Ishaq ya ce, “Amfanin da muke da shi a wannan tattaunawa ta zaman lafiya shi ne rasuwar marigayi Abubakar Shekau da kuma yadda jama’a ke da qudurin yin haquri su zauna tare da waɗannan ’yan ta’addan wuri guda.

“Sun yi gargaɗin cewa babu wanda ya isa ya amsa kiran wajen tattaunawar matuƙar sun san da haka take za su kashe wanda duk suka samu da hakan, a zahiri kan hakan sun kashe mayaƙansu sama da 300 da iyalansu da ke fitowa daga dajin na Sambisa,” inji shi.

A cewarsa, ko a makon da ya gabata sai da ’yan ƙungiyar suka kashe wasu kwamandoji uku da iyalansu da ke shirin tserewa don miƙa wuya, inda ya ce hakan ya jima yana faruwa.

“Don haka duk wani ɗan Boko Haram da ya miƙa wuya da ka gani a sansanin a yanzu to kasada da ransa ya yi ya fito. Abin takaici ne yadda kwamandojin ke kashe yara, mata da nakasassu da suka fahimta na shirin tserewa ne daga cikinsu.

“Har wayau a makon da ya gabata ma aka samu wani bidiyo da suka sanya jajayen kaya a jikinsu, wadda Amir ne ya amince da fitar su amma abin takaici an halaka su don sanya tsoro ga waɗanda suke son miqa wuya,” inji Birgediya Janar Ishaq.

Sai dai ya alaqanta irin nasarar da ake samu a kan ’yan ta’addan da addu’o’in da al’ummar Borno suka yi da kuma manufofin siyasa na gwamnati mai ci a jihar.