INEC za ta yi haɗaka da ƙungiyoyin sufuri kan zirga-zirga ranar zaɓe

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da lokacin babban zaɓe yake ƙara ƙaratowa, Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta (INEC) ta haɗa gwiwa da direbobi, mamallakan motocin haya, da sauran ma’aikatan tashar mota a jihar Oyo domin a samo hanyar da za a tafiyar da hada-hadar sufurin mutane da kaya a ranar zaɓe mai zuwa. 

Wannan shi ne dalilin da ya sanya hukumar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki don tattaunawa a kan haka. 

Dakta Adeniran Tella, Bature Zaven na jihar Oyo (REC) da kuma INEC, su suka sanar da haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ganawa da shugabannin ƙungiyoyin sufuri a ranar Talatar da ta gabata a Ibadan.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan taro ya samu halartar ƙungiyoyin sufurin mota da suka haɗa da ƙungiyar direbobi ta NURTW, da ƙungiyar mamallakan Ababen hawa da ake haya da su ta NARTO, da qungiyar RTEAN, da shugabannin gudanarwa na tashar Oyo, wakilan hukumar tsaro na farin kaya (DSS), da sauransu.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa, a taron ganawar an samu an cimma matsaya da ma’aikatan sufurin motocin ta yadda aka tsara yadda hukumar INEC za su samu halarta wuraren zaɓen da wurwuri ranar zaɓe. 

A cewarsa, matsalar sufuri a kullum shine babbar matsalar da ke kawo tsaiko wajen halartar ma’aikatan zave zuwa wurin zaɓen akan kari. 

A don haka a cewar sa, hukumar ta zauna da direbobin da sauran masu ruwa da tsaki domin a cimma matsaya a kan iya adadin Ababen hawa da ake buqata a kowacce ƙaramar hukuma a ranar zaɓe. Kuma za a ba da bayani da cike takardu na mambobinsu ko da wata matsala za ta afku.

Sannan kuma bayan haka a cewarsa, za a samar da wani kwamiti mai ɗauke mutane guda uku da za su wakilci kowacce ɗaya daga ƙungiyoyin direbobin, da mamallakan motocin haya da kuma ma’aikatan tasha sannan da wakili ɗai-ɗai daga INEC da sauran masu ruwa da tsaki, waɗannan mutane za su cigaba da yin taro a kai-a kai don samar da sufuri maras tangarɗar a ranar zaɓe.

Sannan kuma ya bayyana cewa, za a tabbatar da kowanne abin hawa hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) ta caje shi tsaf, don tabbatar da lafiyarsa. Kuma sannan hukumar ba za ta yarda da duk wani abin hawa da yake ɗauke da alama ko tambarin wata jam’iyya ba ko wani abu na qashin kai a ranar zaɓen ba. 

Wannan haɗakar dai ta samu goyon bayan Kwamishinan ‘Yansanda na jihar Oyo, Adebowale Williams, wanda ya bayyana cewa, da ma taimakawa wajen yin zaɓe cikin nasara aikin kowanne ɗan ƙasa ne. Kuma ya shafi direbobin da sauran masu ruwa da tsaki. Haka hukumar FRSC ta jihar, Oyo, ta bakin shugabanta Olalekan Morakinyo, ta bayyana cikakken goyon bayanta.