Chelsea ta kai zagayen daf da kusa da ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Chelsea ta farfaɗo da fatanta a kakar wasan bana, bayan da ta doke Borussia Dortmud da ci 2 da nema a karawar da suka yi a Stamford Bridge, inda a yanzu ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar zakarun Turai.

Raheem Sterling ne ya fara jefawa Chelsea ƙwallo kafin Kai Havertz ya jefa ta biyo a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Mai horar da ƙungiyar Graham Potter na fuskantar matsin lamba bayan da kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu, ganin yadda ƙungiyar ta kafa tarihin yawan kashe kuɗi wajen sayen ’yan wasa har Euro miliyan ɗari 5.

An jinkirta fara wasan da minti 10 saboda cin karo da cinkoson ababen hawa da tawagar ta Dortmund ta yi a birnin London.

A wasan farko da ƙungiyoyin suka yi a Jamus, Dortmund ce ta samu nasara da ci ɗaya mai ban haushi, inda ta zo wasan na jiya cike da fatan samun nasara don kaiwa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe.