Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotu ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga

Daga WAKILINMU

Kotun Ƙoli ta maye sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau da na Rufai Hanga a matsayin zaɓaɓɓen Sanata na Kano ta Tsakiya karƙashin Jam’iyyar NNPP.

Da yake yanke hukunci kan ƙarar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ɗaukaka kan hukuncin da Babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta yanke da farko, Alƙalin Koton Ƙolin ya tabbatar da Hanga a matsayin ɗan takarar NNPP.

Tun farko, Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara sun tabbatar da Rufai Hanga a matsayin Ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar NNPP biyo bayan janyewa da Ibrahim Shekarau ya yi a matsayin mamba da kuma ɗan takara a jam’iyyar.