Cinikin motoci a ƙasar Sin ya ƙaru zuwa kaso 23.8 a watan Yuni

DagaCMG HAUSA

Ƙungiyar masu kera motoci ta ƙasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, yanayin sayen motoci a ƙasar Sin ya ƙara samun tagomashi a cikin watan Yuni, tana mai alaƙanta hakan da raguwar ɓarkewar annobar COVID-19 da ingantattun manufofi.

Alƙaluman ƙungiyar sun nuna cewa, an sayar da jimilar motoci miliyan 2.5 a cikin watan Yuni, adadin da ya ƙaru zuwa kaso 23.8 a kan na shekara guda da ta wuce.

Fassarawar Fa’iza Mustapha