Tattalin arziki mai alaƙa da fasahohin zamani na samun cigaba a ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA

Fannin tattalin arziki mai alaƙa da fasahohin zamani ya shafi zaman rayuwar dukkanmu. Duk wani lokaci da muke biyan kuɗi da wayar salula, ko kuma sayen kayayyaki ta kafar yanar gizo na Internet, muna samar da gudunmowa ga ci gaban wannan fanni na tattalin arzikin.

Yanzu haka, wannan ɓangaren tattalin arziki na samun ci gaba cikin matuƙar sauri a ƙasashen Afirka. Idan mun ɗauki ɓangaren kasuwanci ta kafar shafin Internet a matsayin misali. Mutanen da suka sayi kaya ko kuma suke yin ciniki ta kafar Internet sun kai miliyan 233 a ƙasashen Afirka a shekarar 2019, adadin da ake sa ran ganin ƙaruwarsa zuwa miliyan 478, zuwa shekarar 2024. Wannan yanayi na samun ci gaba ya burge mutanen duniya, kana wani abun da ya fi sa ni murna, shi ne yadda fasahohi na ƙasar Sin ke taka muhimmiyar rawa a ciki.

A kasar Kenya, mutane sun fara yin amfani da manhajar da ake kira “Mobile Wallet” wajen biya kuɗi a shekarar 2007. Wannan manhajar ta sa mutane suna iya biya da karɓar kuɗi, ta hanyar tura sakon text, ko da kuwa wayoyin salularsu ba na zamani ba ne. Sai dai, wannan fasaha ta gamu da matsala a shekarar 2012: Yadda ake samun ɗimbin mutane masu yin amfani da manhajar ya sa aka ƙasa tafiyar da ita yadda ake buƙata, inda aka fara gamuwa da matsalar karɓar kudi duk ranar Juma’a.

Don daidaita wannan matsala, an gayyaci wani kamfanin ƙasar Sin, wanda ya taimaka wajen inganta manhajar zuwa wata da ba za a sake gamuwa da matsala yayin da ake amfani da ita ba, har ma an kara wasu hidimomi na sayen tikitin jirgin sama, da na kasa a ciki. Zuwa yanzu, manhajar “Mobile Wallet” ta samu mutane masu yin amfani da ita kimanin miliyan 30 a ƙasar Kenya, da sauran wasu fiye da miliyan 20 a ƙasashen Tanzania, da Ghana, da Masar, da dai sauransu.

Haƙiƙa muna iya ganin yadda haɗin gwiwar Afirka da Sin ke tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai alaƙa da fasahohin zamani a ƙasashen Afirka, a fannoni daban daban. Misali, a fannin kasuwanci ta kafar Internet, wani dandalin kasuwanci da wani kamfanin ƙasar Sin ya kafa, yana taimakawa wajen samar da kayayyaki na ƙasashe daban daban, zuwa mutane kimanin miliyan 300 na gabashin Afirka, da samar da guraben aikin yi ga mutane fiye da dubu 10.

Kana a ɓangaren horaswa, kamfanonin ƙasar Sin sun yi hadin kai da jami’o’in ƙasar Afirka da Kudu, wajen kafa cibiyoyin nazarin fasahohin sadarwa na zamani. A cewar Abdullahi Usman, darektan sashen raya kayayyakin more rayuwa na hukumar raya fasahohin sadarwa na zamani a Najeriya, yanzu a wasu birane 17 dake wasu ƙasashe 15 na nahiyar Afirka, akwai kamfanoni fiye da 1500 da suke ƙoƙarin haɗin gwiwa da kamfanonin ƙasar Sin wajen shigo da fasahohi na zamani.

Yadda waɗannan kamfanonin ƙasashen Afirka suke ƙoƙarin haɗin gwiwa da kasar Sin ba zai ba mutane mamaki ba. Kasancewar shirin raya fasahohin zamani na cikin manyan yarjeniyoyin da ƙasashen Afirka suka ƙulla tare da kasar Sin, yasa an ƙarfafa haɗin gwiwar bangarorin 2, har zuwa shekarar 2035. Wannan shiri ya dace da manufar ƙasar Sin ta “koya wa mutane fasahar kamun kifi maimakon ba su kifi kawai” a fannin hadin gwiwarta da ƙasashen Afirka, kana zai biya buƙatar ƙasashen Afirka ta zamanintar da fasahohi, da raya tattalin arziki.

A yanzu mun fara ganin sakamakon shirin, kana za mu ga karin nasarorin da za a samu ƙarƙashinsa a nan gaba.

Fassarawar Bello Wang