Ciwon daji

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa barkan mu da wannan lokaci, sannun mu da jimirin gudanar da al’amuran rayuwa. Ya mu ka ji da zafi? To Allah ya ba mu wucewa lafiya.

In sha Allah yau za mu yi magana akan ciwon kansa ko daji ko kansa. Zan mayar da hankali wajen kawo abubuwa da ke jefa mutum cikin haɗarin kamuwa da cutar da kuma hanyoyin da za a bi wajen rage afkwawa cikin haɗarin  kamuwa da ita.

Amma kafin mu fara, Ina son mu fahimci cewa, babu abu ɗaya tilo da ke jawo ciwon kansa; abubuwa ne da yawa waɗanda idan su ka ci karo da juna to sai cutar ta afku.

Hadarin kamuwa da ciwon kansa:

Akwai abubuwa da ke jefa ɗan adam cikin haɗarin kamuwa da wannan ciwo. Ga wasu daga ciki kamar haka:

1. Shekaru

2. Jinsi

3. Zuƙar taba

4. Shan giya

5. Gado

6. Muhalli

7. Ƙwayoyin cuta

8. Cima maras kyau

9. Magunguna

10. Ƙiba

Idan dai har za ku cigaba da bibiyar wannan shafi, cikin nufin Allah, sannu a hankali zan kawo yadda kowanne daga cikin waɗannan ke da alaƙa da ciwon kansa. Ya na da kyau mu san cewa wasu daga cikin waɗ annan abubuwa da na lissafo, wasu daga ciki babu yadda mutum zaiyi ya sauya su. Misali: shekaru, gado, da jinsi.

Kare kai daga haɗarin kamuwa da ciwon kansa ko daji:

1. Motsa jiki

2. Cima mai kyau

3. Rage ƙiba

4. Gujewa taba

5. Gujewa giya

6. Gujewa sinadarai masu cutarwa

7. Sanin ilimin ciwon (daidai misali)

Ku tara a rubutu na gaba.

By ukarofi