Cutar korona: Shugaba Bio ya kafa dokar hana fita a Sierra Leone

Daga WAKILINMU

A matsayin wani mataki na yaƙi da ɓullar cutar korona karo na uku a ƙasar Sierra Leone shugaban ƙasar, Julius Maada Bio, ya bayyana kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na asuba, wadda za ta soma aiki Litinin mai zuwa idan Allah Ya kai mu.

Ɗaukar matakin ya haɗa har da rufe masallatai da mujami’u, sai gidajen abinci da aka buƙaci su riƙa tashi da ƙarfe 9 na dare, sannan taron bukukuwa kada a wuce mutum 50.

Bio ya bayyana ɗaukar matakin ne a Alhamis da ta gabata, tare da cewa an yi hakan ne domin yin abin da ya kamata a kan kari wajen yaƙi da cutar korona karo na uku a ƙasar da kuma taimaka wa Afirka ta Yamma wajen cin galaba a kan annobar.

A cewar Bio, “Mun yi amannar cewa dole ne mu hanzarta ɗaukar matakin da ya dace don yaƙi da ɓullar annobar korona karo na uku.”

Duk da dai adadin waɗanda suka harbu da annobar a ƙasar kaɗan ne idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe, inda a yanzu ƙasar ke da mutum 5,652 da suka kamu da cutar a faɗin ƙasar, sannan mutum 102 sun mutu sakamakon cutar.

Sierra Leone mai yawan jama’a milyan 7.5, bayanan hukumomin lafiyar ƙasar sun nuna a ‘yan kwanankin nan an samu ƙaruwar masu kamuwa da korona, ganin cewa tsakanin 1 ga Yunin da ya gabata zuwa yau, an samu mutum 1,500 da suka harbu da cutar.