Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Ya na da kyau iyaye mu san mene ne mahimmancin yara da tarbiyyarsu da Allah ya ba mu, ba don komai ba sai don sanin cewa shi ɗa amana ne a gurin iyaye. Ko a cikin fatawa ta addini, malamai sun faɗi cewa, ɗa amana ne ga mu kanmu iyaye mata, don mu san cewa, tarbiyya wata babbar amana ce a gurinmu, saboda mace ita ce ja gaban tafiyar da tarbiyyar ’ya fiye da shi kansa mahaifi.

Dalili shi uba sabgoginsa kaɗan ne cikin gida, saboda fita nema ga iyali na sanya sa idonsa akan ‘ya’ya bai kai na uwa ba, wacce ita tana gida kuma tana tare da yaran. Dole ita ce mai kula da sa ido akan rayuwar da suke gudunarwa.

Yanzu komai ya canja, ba kamar da ba da ko harara uwa ta yi wa yaro, ya san me ta ke nufi, kuma zai tsorata ya kasa maimaita abun da ya ke yi, sa~anin na yanzu da ko da idon uwa zai faɗo ɗasa, ba zai fasa abun da ya ke yi ba. 

Tarbiyya: Tarbiyya zaman kanta ta ke yi, domin duk inda aka ambace ta ma an san wani nau’i ne na gaske da ake so a kiyaye shi. Yanzu son rai ya fi yawa a cikin al’umma; babu ƙarfin da ake ba wa yara irin na su san daidai da rashin daidai. A da maƙoci ma zai iya hukunta ɗan maƙocinsa, saɓanin yanzu da hakan ba za ta taɓa samuwa ba.

Uwa na gani ɗa na aikata aiki na rashin tarbiyya, amma ba za ta hana ba har ya aikata abun da shi a gurinsa daidai ne. To, muddin yaro ko zai yi ɓarna, uwa ko uba ya sa masa ido, ba tsawatarwa, gobe ma zai aikata fiye da haka da sunan shi daidai ya ke yi. Daga haka ya zame masa jiki kuma hakan zai sa ya tashi babu tsoro, babu shayin abin da yayi ɗin ba mai kyau ba ne.

Itace tun yana ɗanye ake tanƙwasa shi: Na sha jin wannan kalmar a gurin iyayenmu, amma na nemi amsa na rasa sai da na girma na ajiye nawa, na san me ake nufi, wato muddin za ka sa wa ɗanka ido ya yi yadda ya so, to ba shakka akwai gagarumin giɓi a raruwarsa da iyayen ma, domin shi dambu da ma an ce idan ya yi yawa, bai jin mai. Muddin ]a zai aikata laifi yau, ya yi gobe, babu kwaɓa, to lokacin da ka ke son dawo da shi hanya, shi kuma ya riga ya yi nisa, ba fa zai dawo ba.

Shi ɗa kamar lawashi ne; idan ya bushe, to tashinsa sai an shirya, amma idan ya kauce, aka dawo da shi hanya tun da wuri, aka nuna masa meye baƙi da fari, to dole zai gane cewa, abun da ya yi ba mai kyau ba ne. Sai ya zamo ya yi koyi da abin da iyaye ko ma wani ya faɗi ma sa, amma muddin zai yi kuskure ya rasa mafaɗi, to tashi zai zama ɗan kansa, wato babu mai sa shi ko hana shi. Daga nan tarbiyya ta yi tawaya.

Yana da kyau iyaye mu duba yadda muke da yaranmu, mu kuma san me suke yi a gida ko a waje, don yanzu kana gidan ma ɗan zai aikata fitina ba tare da iyaye sun sani ba, sai bayan ya faru za ka san ka yi babban kuskure; kuskuren da dawowa hanya zai yi matuƙar wahala.
 
Abokai da iyaye su sa ido kan yaransu da wanda suke mu’amala da su. A san waye yaro ko yarinya ke bi ko suke haɗuwa tun kafin lokaci ya ƙure. 

A makon gobe da yardar Allah za mu ɗora akan wacce irin illa abokai ke yi ga yaranmu; wacce irin gudunmawa suke ba dawa cikin rayuwar yaranmu yadda za mu kiyaye hakan. A tara da mu sati na gaba, idan Allah ya sa muna raye.

Ƙofa a buɗe ta ke ga masu neman shawara ko gyara akan wannan shafi na Fagen Tarbiyya.