Tare da CHIROMA AMINU ASID
1. Ciwon Suga nau’i na ‘Type 2 Diabetes’: Ana iyawa warkewa daga wannan ciwon idan yana matakin farko ta hanyar rage kiba, motsa jiki, cin ganyayyaki da rage shan lemo mai gas.
2. Hawan Jini a Farkon Faruwar Sa: Shima ana iya warkewa ba tare da shan magani ba ta hanyar rage cin gishiri, shan taba da barasa idan mutum yana yi, motsa jiki, sarrafa damuwa, da rage ƙiba.
3. ‘Cholesterol’ mai yawa: Idan cholesterol yayi yawa ba mai tsanani sosai ba, ana iya rage shi ta hanyar cin abinci mai rage cholesterol kamar hatsi, kifi, yayan itatuwa da ganyayyaki. Tare sa rage cin abin Mai yawan mai da danyen kitse sanan da motsa jiki.
4. Rashin barci (Insomnia): Rashin bacci na wucin gadi ana magance shi ne ta hanyar amfani da “sleep hygiene” kamar rage amfani da waya kafin barci, daidaita lokaci na barci da farkawa), age damuwa ta hanyar natsuwa, addu’a da karatun Qur’an.
5. Ciwon ciki sakamakon damuwa ko bacin rai (Stress-induced Ulcers or IBS – Irritable Bowel Syndrome): Shima ana warkewa ta hanyar canza kalar abinci, aarrafa damuwa, atisayen natsuwa kamar yoga exercise.
6. Ciwon baya: Ciwon baya a matakin farko ana iya magance shi ta hanyar motsa jiki a hankali, gyara zama da kwanciya, rage nauyin jiki da neman taimakon physiotherapy.
7. Kiba (Obesity): Ana iya rage ta ta hanyar yin atisaye a ƙalla na minti 30 zuwa 60 a rana, rage abinci mai kitse, cin abinci mai cike da fiber, yayan itatuwa da ganyayyaki, rage shan lemo da abinci mai zaƙi, samun barci mai kyau da rage damuwa (stress).
8. Ciwon Kai (Migraines ko Tension Headaches): Shima ana magance shi ta hanyar gujewa abubuwan da ke haddasawa kamar cheese, caffeine, ko rashin barci, rage damuwa ta hanyar tafiya, yoga exercise, cin abinci a kan lokaci, wadataccen bacci, da motsa jiki na yau da kullum.
9. Ciwon Zuciya Na Matakin Farko: Ana magance shi ta hanyar cin nau’in abinci kamar hatsi, kifi, da ‘ya’yan itatuwa, motsa jiki, rage kiba, rage damuwa da barin shan taba sigari.
10. Ciwon Asma (Mild Asthma): Ana magance shi ta hanyar gujewa kura, hayaƙi, age kiba (idan akwai), cn abinci mai daɗa lafiya, motsa jiki mai sauƙi da kula da sauyin yanayi da iska.
11. Ciwon Ƙoda a Matakin Farko: Ana magance shi ta hanyar rage cin gishiri da abinci mai kitse., ujewa abinci mai yawan sinadarin phosphorus da potassium, shan ruwa yadda ya kamata, barin shan magunguna da za su iya lalata ƙoda ba tare da kulawar likita ba (Magungunan gajiya da sauransu).
12. Ciwon ciki da tari: A matakin farko ana magance shi ta hanyar gujewa abinci mai gishiri, mai, da acid (kamar tumatir da lemon tsami), rage kiba, tsayawa tsawon lokaci bayan cin abinci kafin kwanciya, da Kuma cin abinci kadan-kadan sau da yawa a rana.
Abin lura:
Ana iya magance cuta ne idan bata kai wani mataki mai tsanani ba. Idan kuma tsanani, to magani ko kulawar likita na da muhimmanci fiye da wadannan din. Kuma kada a watsar da shawarar likita in anfara samun sauƙi.
