Tarihin Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami (1943-2025)

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An haifi Muhammed Sani Sami a Zuru, Jihar Kebbi, a ranar 24 ga Oktoba, 1943. Ya shiga Rundunar Sojin Najeriya a ranar 10 ga Disamba, 1962, inda ya samu horo tare da Ibrahim Babangida.

Daga bisani ya halarci Mons Officer Cadet School da ke Aldershot, Ingila, inda ya zama jami’i a ranar 25 ga Yuli, 1963.

Ya halarci yakin basasa na Najeriya, kuma ya jagoranci dakarun da suka fatattaki sojojin Chadi da suka kutsa Jihar Borno.

A watan Yuli 1975, Janar Murtala Mohammed ya naɗa shi kwamandan Brigade of Guards a matsayin Lieutenant Colonel.

Bayan juyin mulkin 31 ga Disamba, 1983 wanda ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki, an naɗa Sani Sami a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Bauchi.

Ya riƙe wannan muƙamin har zuwa watan Agusta 1985 lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya karɓi mulki daga hannun Buhari.

A lokacin mulkinsa a Bauchi, ya inganta cibiyoyin lafiya tare da kaddamar da babban shirin noma mai taken “Back to Land.”

Haka kuma ya jagoranci shirya gasar cin kofin duniya ta wasan handball a jihar.

A watan Oktoba 1984, lokacin da ake fuskantar ƙaruwa na matsalolin addini, Sani Sami ya jaddada haramcin wa’azin addini a fili.

Ya kuma bayyana cewa rushe wasu coci-coci domin gina sabon ring road ba ya nufin hari ne kan addinin Kirista, tare da ƙara da cewa gwamnati ta ware fili domin Katolika su gina sabon coci.

Ya yi ritaya daga rundunar soji a matsayin Manjo Janar a ranar 3 ga Satumba, 1990. A shekarar 1995, aka naɗa shi Sarkin Zuru na 11, mukamin da ya riƙe har zuwa rasuwarsa.

Sarkin Zuru, Alhaji Mohammed Sani Sami Gomo II, ya rasu a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke birnin London bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 82.

By ukarofi